Hong Kong za ta tsaurara dokokin tsaron kasa
January 30, 2024Gwamnatin Hong Kong ta sanar da cewa za ta samar da sabuwar doka a cikin dan gajeren lokaci da ta jibanci tsaurara dokokin tsaron kasa da za a saka a cikin kundin dokokin da China ta shinfida a shekarar 2020.
Karin bayani: An kafa cibiyar tsaro a Hong Kong
Wadannan sabin dokoki za su kunshi tanade-tanade guda biyar ciki har da cin amanar kasa da tayar da kayar baya da kuma leken asiri, a fadar wadansu manyan kusoshi na gwamnatin Hong Kong ciki har da John Lee shugaban zartarwa na yankin da ke Kudancin China. Mr Lee ya kuma kara da cewa wannan mataki wani mahinmanci abu ne ga tsarin mulkin na Hong Kong wanda ba a ka'ide shi ba a lokacin da Burtaniya ta hannata wa China yankin shekaru 26 da suka gabata. Tuni ma dai in ji shi aka fara shirya tsarin tuntubar juna kan daftarin wannan sabuwar doka wadda za ta kara karfafa tsaro a wannan yanki na China da ke karkashin tsarin kasa daya mai amfani da tsarin shugabanci biyu.
Karin bayani: China: Na'am da dokar tsaro a Hong Kong