Najeriya: Samo riba ga kamfanin NNPC
January 7, 2022NNPC dai na zaman kamfani daya tilo da ke tsakiyar harkar man fetur, kuma ke kirga asara a shekara a duniya baki daya. Kafin kai wa ya zuwa wata dokar masana'antar man fetur da ke zaman irinta ta farko, kuma ke neman sauyin lamura a daukacin masana'antar. Gwamnatin Najeriyar dai ta kaddamar da wata hukuma ta gudanarwar da Abujar ta dorawa alhakin tafi da harkokin kamfanin, domin neman riba da goga kafada da 'yan uwansa a duniya baki daya. Kuma shugaba Buhari bai boye fatan kasar na sauyin tako daga matattarar wasoson 'yan mulki zuwa ga kamfanin da 'yan kasar ke iya takama da shi nan gaba ba: "Kaddamar da hukumar mataki ne babba, a kokarin tabbatar da ingantacciyar masana'antar man fetur da ke iya jawo masu zuba jari na waje da gina tattalin arzikin kasa da samar da aikin yi ga miliyoyi na 'yan kasar. Ana sa ran kamfanin NNPC, zai bi ingantattun ka'idojin kasuwanci da ke dora fifiko kan bin dokoki da kaucewa nuku-nuku a cikin harkokinsa."
A bara kadai dai kuma a karon farko a shekaru 44, kamfanin ya sanar da ribar da ta kai Naira miliyan dubu 287. Najeriyar dai na fatan kara moriya daga NNPC da kasar ta dauki lokaci tana yi wa kallon ceto, amma kuma ta kare a cikin bacin rai. Bacin ran da ya kalli tayar da hankali daga al'ummar yankin, ya kuma kai ga fara ficewar kamfani mafi girma na Royal Dutch Shell daga yankin Niger Delta. To sai dai kuma mai da kasuwar zuwa alkali da ya fara daga shekarar da ta shude dai, a fadar Mele Kyari da ke zaman shugaban kamfanin ya fara nuna alamun tasiri a kokarin tabbatar da kamfanin abun alfaharin 'yan boko da kila ma talakawan Najeriyar. Gaza tasirin NNPC dai na da ruwa da tsaki da gazawar 'yan mulki na kasar da ke dogaro da harkar man, amma kuma ke kallon raguwar kudin shiga duk da karuwar farashin man fetur din a duniya. Har ya zuwa yanzu makomar tallafi na shirin zama karfen kafa a tsakanin mahukuntan da ke kallon zare tallafin a matsayin mafitar kara samun kudi ga hukuma da kuma masu kwadagon kasar da ke kallon kokarin matsa lamba ga 'yan kasa. Duk da tashin farashin man da ya haura dalar Amirka 80 kan kowace ganga, kamfanin ya rika bayar da gudummawar da ba ta taka rawa ba sakamakon matsalar tallafi da ke cinye riba. To sai dai kuma a fadar Simon Lalong da ke zaman gwamnan jihar Plateau kuma shugaban gwamnonin arewacin Nnajeriyar, 'yan kwadago suna shirin daukar hakuri ga batun zare tallafin da ke iya amfanar kowa. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kaya wa, a tsakanin masu takama da neman araha da sunan tallafi da kuma masu tunanin sauyi da nufi ci-gaban al'umma.