Barazana mai girma ga tattalin arzikin Najeriya
April 29, 2021Duk da cewar dai mahukuntan kasar na tsallen murnar tashi na farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya, a gefe daya dai tallafin tattace man da kasar ta dauki lokaci ta na shigo da shi na barazana ga makoma ta kasar da ke dogaro da bakar hajjar man.
Wata wasikar da kamfanin man NNPC ya aike zuwa ga babban akawun kudi na gwamnatin tarraya dai ta ce, a watan Mayun da muke shirin shiga har ya zuwa Yulin da ke tafe dai kada gwamnatoci a matakan kasar guda Uku su sa ran samun kudi daga kamfanin da ke zaman saniyar tatsa ga kasar.
Wasikar dai ta ce a cikin watan Afrilun da muke ciki dai kamfanin ya biya abun da ya kai Naira miliyan dubu 111 da sunan tallafin man fetur da 'yan kasar suka sha a wata daya tilo.Najeriya.
Karin bayani: Najeriya: Hanyoyin fita daga matsalar kudi
Abun kuma da ya cinye daukacin gudummowar kamfanin ga kudade na rabo a tsakani na matakan mulkin kasar guda uku.
A yayin da farashin man fetur ke sauka a tashar jirgi na ruwa a farashin da ya kai Naira 184 kan ko wace lita daga waje, kamfanin na bada shi ga masu dillanci kan Naira 126. Abun da ke nufin ragin da ya kai na kusan Naira 60 kan ko wace lita ga kasar da ke shan lita Miliyan hamsin da doriya a kusan kullum.
Wannan ne dai karo na farkon fari da tasiri na tallafin ke kara fitowa fili cikin kasar da ke tsaka mai wuya a samar da kudade na biyan albashi da aiyyukan yau dana gobe.
Karin bayani: Matatun mai masu zaman kansu a Najeriya
Koma ta ina ake shirin abi da nufin kaiwa ya zuwa samun tsira ga a'in da ke rama a halin yanzu, kasa da jihohin kasar guda biyar ne dai ke iya rayuwa ba tare da dogaro ga kudin shigar man fetur da harajin na Abuja da ake rabawa a duk wata a Abuja.
Tarayyar Najeriyar dai na fatan fara aiki na matatar man fetur din Dangote a shekarar da ke tafe, na iya rage radadin rikicin ga kasar da ke karba da hagu sannan kuma ta mika a cikin hannun dama a cikin harkar man fetur.
Karin bayani: Najeriya ta sake shiga matsin tattalin arziki
Matatar da ke zaman irinta mafi girma a duniya dai zata samar da litar mai dubu 650 a kusan kullum, ko bayan sai da man da Naira ta kasar.