1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar kamfanin NNPC a Najeriya

August 18, 2021

Duk da adawa daga sassa dabam-dabam na Tarayyar Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamitin da ya dorawa alhakin aiwatar da sabuwar doka da ka iya yin tasiri ga makomar masana'antar man kasar.

https://p.dw.com/p/3z8bE
BG Regierungssitze | Abuja
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCHoto: Reuters/A. Sotunde

Kama daga gwamnoni na jihohi ya zuwa al'ummar yankin Niger Delta da ke samar da daukacin man fetur na kasar dai, adawa tai nisa kan sabuwar dokar da shugaban kasar ya rattaba hannu a kanta cikin wannan mako. To sai dai kuma Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar, ya  yi wurgi da adawar ta hanyar fara aiwatar da sabuwar dokar da gwamnatin kasar ke fatan ka iya mai da tsohuwa yarinya cikin masana'antar. Buharin cikin wani jawabi da ya yi ga 'yan kasar a Abuja fadar gwamnati, ya bai wa wani kwamiti karkashin karamin ministan man fetur na kasar tsawon watanni 12, domin aiwatar da baki dayan tanadin dokar da sannu a hankali ya tabbatar da 'yancin masana'antar daga hannun gwamnati.

Karin Bayani: Matatun mai masu zaman kansu a Najeriya

Shugaba Buharin bai boye ba, kan umartar ma'aikatu da hukumomin gwamnati da su bayar da hadin kai domin kai wa ya zuwa nasarar da kasar ke fatan samu daga masana'antar. To sai dai kuma shugaban ya dau 'yar lallashi da nufin shawo kan  al'ummar da ake hakar albarkatun man fetur din a yankunansu da kuma suka sa kafa domin shure kaso uku cikin 100 na kudin man da doka ta tanadar domin amfaninsu. "Ina rokon al'ummar da ke samar da man fetur da iskar gas da su yi kallon tsaf, kan dokar da aiwatar da ita ka iya samar musu da ci-gaba mai dorewa. Ko bayan nan dai dokar ta kuma tanadi kai karshen kona iskar gas da zai bayar da damar samun gudummawar Najeriya ga yarjejeniyar birnin Paris ta muhalli, ta samar da kudi domin kai karshen kona iskar gas a cikin yankin."

Niederlande Den Haag | Protest gegen Ölverschmutzung durch Shell in Nigeria
Jihohin da ake hakar man fetur a Najeriya na fama da gurbatar muhalliHoto: Mike Corder/AP Photo/picture alliance

Haka kuma dokar ta samar da damar sauyi ya zuwa ga makamashi mai dorewa da duniya ke yayi. Sannan kuma ta tanadi dama ga kamfanin mai na kasar NNPC na zuba jari a harkar makamashin mara illa. Domin dorawa a kan imanin wannan gwamnati na samun ci-gaban da dokar ke burin cimmawa, shugaban ya ce ya amince da kafa majalisar zartarwa domin fara aiki nan take. Kwamitin a karkashin karamin ministan man fetur, zai kamalla aiwatar da wannan doka a cikin watanni 12. Ko bayan masu samar da man da ke fadin ta lalace, su kansu jihohi na kasar dai na kallon dokar a matsayin kokari na rage kudin shigar da suke samu baya ga rage tasirinsu cikin masana'antar man da ke zaman saniyar tatsar kowa.

Karin Bayani: Karancin man fetur na janyo cikas a Najeriya

Tun a cikin makon jiya ne dai, gwamnonin suka aikewa shugaban kasar da wata wasika da a cikinta suke neman da ya jinkirta rattaba hannun. Kuma majiyoyi ma sunce suna shirin tunkarar kotu, kafin shigar sauri ta shugaban da ta barsu da kumfa a baka. Sanata Ahmed Lawal  dai na zaman shugaban majalisar dattawan Najeriyar da kuma ya jagoranci kafa dokar da ke zaman gada da fata na kokarin yanke talauci. A cewarsa lokacin da ke tafe, na zaman na yin adalci a tsakanin kowa cikin kasar. Ana sa ran rushe tsarin kamfanin man NNPC da ke da babakere na hukuma cikin tsawon wattani shidan da ke tafe, tare da maye gurbinsa da sabon tsarin da zai kalli riba a fadar shugaba na kamfanin na NNPC Mele Kyari.