Jamus za ta zuba jari a kan makamashi a Najeriya
November 22, 2023Tun bayan hawansa karagar mulki a watan Mayu, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke zawarcin masu zuba jari daga kasashen waje zuwa ga kasar da ke da mafi karfin tattalin arziki a Afirka yana mai nuni da sauye-sauyen da ya yi kan tallafin man fetur da sarrafa kudaden a matsayin abin karfafa gwiwa.Tinubu ya je Berlin ne domin halartar taron hadin gwiwa na tsakanin Berlin da kasashen Afirka mai suna G20 Compact with Africa. Kamfanin Riverside LNG na Najeriya da ke aiki a yankin Niger Delta da takwaransa na Jamus mai harkar makamashi na Johannes Schuetze Energy Import ne suka rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar juna kan yarjejejiyar ta samar wa Jamus iskar gas. A cewar shugaban na Najeriya dai demokradiyya ta samu gindin zama a wannan kasa mai mafi yawan al'umma a Afirka, kuma hakan na nuni babu wata fargaba ka wadanda ke son zuba jari a kasar duba da dumbin albarkatu da Allah ya hore mata...Tinubu: " Kuna da zabi, noma na daya daga cikin sassan da ke bunkasa a Najeriya, kazalika bangaren makamashi. Za ku dora daga inda muka tsaya. A bangaren ilimi kuwa muna da yara matasa masu basira da hazaka da za ku iya horarwa, don haka muna iya musaya ta yadda duk za mu samu ci gaba"
Za a samar da makamashi daga Najeriya zuwa Jamus kan tan 850,000 a duk shekara
Shugaban kamfanin GasInvest, daya daga cikin abokan huldar Najeriya da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar junan David Ige, ya ce aikin zai samar da makamashi daga Najeriya zuwa Jamus kan tan 850,000 a duk shekara, wanda zai fadada zuwa tan miliyan 1.2 a duk shekara. Ana sa ran iskar gas na farko zai bar Najeriya a shekarar 2026. Sanarwar ta ce an sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta kunshi alkawarin dala miliyan 500 na ayyukan samar da wutar lantarki a Najeriya, da nufin kawo karin mutane cikin harkar bunkasa tattalin arziki na kasar. Debra Egerue ta kungiyar 'yan kasuwar Jamus da ke Najeriya, bisa dukkan alamu Najeriya ta shirya tsab domin cire kanta kitse a wuta a hanyar bude kofofinta wa 'yan kasuwar Jamus su zuba jari a fannoni daban daban: " Fannin hada hadar kasuwanci na sauyawa, muna da sabuwar tagawa a karkashin shugaban kasa. Kuma daga abun da muka gani na sauye sauye a kasar, akwai fatan cewar kwalli na shirin biyan kudin sabulu, kuma muna fatan hakan".
Yarjejeniya da kamfanin Siemens don taimaka wa Najeriya a fannin wutar lantarki
Har ila yau Jamus na tattaunawa da wata yarjejeniya da kamfanin Siemens na taimaka wa Najeriya a fannin wutar lantarki, wanda tsawon lokaci aka gaza cimma shawo kansa, kuma ya zame wa gwamnati da 'yan kasuwa karfen kafa. A cewar shugaban Comoro kuma wanda ke rike da zagayen jagorancin kungiyar Tarayyar Afirka Azali Assoumani dai, saka hannun jari a tsakanin kasashen Afirka na da matukar muhimmanci. Shirin hadakar na da nufin samar da babban jari mai zaman kansa a Afirka, wanda shiri ne da ya hada kasashen Afirka 13 tare da wakilai daga manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na kungiyar G20 da bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya da bankin raya Afirka. Kuma mahalarta taron na Berlin daga kalamansu, sun nuna sha'awar da 'yan Afirka ke da shi na fadada dangantakarsu a fannin kasuwanci da wasu kasashe ciki har da Jamus.