Isra'ila ta halaka Falasdinawa 200 kafin ta kubutar da hudu
June 9, 2024A jiya asabar, Isra'ila ta yi shelar kubutar da mutum 4 daga cikin wadanda kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a gidan rawa na Nova da ke Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda hakan ya haifar da mummunar yakin da ake gwabzawa tsakanin bangarorin biyu.
Kayan tarihi: Amurka da Burtaniya da Jamus na fatan dakatar da yakin Gaza
Sanarwar Hamas na mutuwar fararen hular na zuwa ne a daidai lokacin da Cibiyar Tattara Bayanan Tsaron Amurka ta sanar da cewa an fara shigar da kayayyakin agajin jinkai a zirin Gaza tare kuma da sake gina tantuna na wucin-gadi a zirin domin sake tsugunar da dubun dubatar 'yan gudun hijrar da suka rasa muhallansu tare kuma da samar da cibiyar tattara kayayyakin agajin jinkan ga fararen hula.
Kayan tarihi: Kotu ta umarci Isra'ila ta dakatar da yaki a kudancin Gaza
A gefe guda, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce sun rasa ma'aikata 135 a yakin na Gaza, adadi mafi girma da aka taba kashe ma'aikatan majalisar a yaki gudu, adon haka akwai bukatar kawo karshen wannan tashin hankalin.