1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabon ango na da tarin kalubale

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 2, 2023

Bayan kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin tarayya a Najeriya, babban kalubalen da ke gaban sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu shi ne yadda zai hada kan al'ummar kasar.

https://p.dw.com/p/4OBRl
Najeriya | Shugaban Kaksa | Bola Tinubu | APC
Zababben shugaban kasar Najeriya Bola TinubuHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

A yanzu dai bayan da aka san waye zai gaji shugaban kasa mai barin gado a Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari na jam'iyya mai mulki ta APC, akwai gagarumin kalubale da ke gaban sabuwar gwamnati ta shugaban kasar mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu. An dai ga yadda kawunan kasar mai yawan kabilu da addinai mabambanta ya rarrabu, a yayin kada kuri'a da kuma bayyana sakamakon zabe. 

Baya ga rarrabuwar kai tsakanin kudanci da arewacin kasar ma kawuna sun rarrabu, inda wasau ke zargin 'yan uwansu 'yan Arewan da rashin hadin kai da kuma nuna keta. Baya ga matsalar rarrabuwar kawuna dama kaksar na fama da tarin matsaloli, kama daga matsalar rashin tsaro zuwa ta tattalin arziki ga kuma ta baya-bayan nan ta karancin kudi.