Sabon farashin wutar lantarki na gigita 'yan Najeriya
April 3, 2024Sabon farashin wutan lantarki da hukumar kula da da harkokin kamfanonin da ke rarraba wutan lantarki ta sanar a Abuja ya nuna cewa gwamnatin ta amincewa kamfanonin su kara kudin wutan ne daga Naira 68 kowane kilowatt na lantarki zuwa Naira 225.
Wannan kari ne da ya shafi mwasu amfani da wutar lantarkin da ke a birane wadanda ke samun wutan lantarki na sao'i 20 a kowace rana, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar kula da sa ido a harkar wutan lantarki Musliu Oseni ya sanar.
Karin bayani : Matakin hana amfani da janareta a Najeriya
Tuni kungiyar kwadagon Najeiyar ta bayyana rashin amincewarta da wannan kari, inda ta ce za ta yi fito na fito da shi.
Hukumar ta bayyana cewa akwai masu amfani da wutan lantarkin da suke a kaso na daya da a yanzu ta mayara da su kaso na biyu saboda gaza cika kaidar samar masu da wutan lantarki.
An yi karin kudin wutar lantarkin ne a daidai lokacin da al'umman Najeriya ke fama da matsaloli na tsadar rayuwa.
Karin bayani : Babban layin wutar lantarki a Najeriya ya sake samun matsala
Gwamnatin Najeriya dai ta dade tana koke cewa ba za ta iya ci gaba da samar da tallafi a kan wutar lantarki da ya kai Naira tirliyan 1.3 ita kuma abinda ta kasafta a wannan shekarar shine Naira bilyan 450.