SiyasaJamus
Bukukuwan tunawa da yakin duniya na biyu
June 5, 2024Talla
A wani gaggarumin hari ta jiragen sama na yaki da na ruwa da dakaru kawance na Birtaninyada Amirka da Rasha suka kadddamar daga Normandi. A daran biyar zuwa shida ga watan yuni na shekara ta 1944, sun kubtar da Faransa daga gwamnatin yan mulkin Nazi na Hitler da kuma wasu sassan dabam-dabam na Turai. Ranar wacce ake yi mata laakabi da sunan D Day, wadda ake bikin cikkar shekaru 80 da yin ta. Yanzu haka an fara kaddamar da bukukuwan tunawa da ita tare da halartan shugabannin Jamus da Italiya da Amirka da kuma sarki Charsle na uku na Birtaniya. Sai dai kasar Rasha wacce ta kasance jagora a yakin da 'yan Nazi a nasara da dakarun kasashen kawance suka samu, wakilanta sun kauracewa bukukuwan