Nijar: Dawo da hulda da kasashe
September 22, 2023
Sannu a hankali dai gwamnatin da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar ta Nijar suka girka na samun karbuwaTakun saka tsakanin Nijar da Faransa a faikace ganin cewa wasu daga cikin kasashen da a baya suka dakatar da ayyukansu domin nuna adawa da juyin mulkin sun soma dawowa inda suke cewa za su ci gabada aiki ne domin al'umma kaman yadda kasar China da farko ta sanar da matsayinta. Sai dai ga masana harkokin kasa da kasa suna ganin tun farko akwai kasashen da ba su cikin masu matsin lamba ga kasar ta Nijar, kamar yada Moutari Ousmane tsohon jami'in diflomasiyya kuma tsohon dan majalisar dokoki na Njar ya bayyana. Sai dai da yake magana daga nasa bangare Alhaji baba Elmakiyya, shugaban kungiyar farar hula ta duniya reshen Turai dan Nijar da ke zama a Nijar da kuma Faransa, ya ce daman sun san haka za ta kasance domin dole kasashe su yi hulda a tsakaninsu, amma kuma sai ya yi kira ga sabbin hukumomin na Nijar da cewa kasashen na waje irin su Faransa ya kamata ne a sake zama a yi sabuwar yarjejeniya da su don gudun komawa 'yar gidan jiya.
Faransa har yanzu ba ta amince ba da sabbin shugabanin mulkin sojoji na Nijar
Ya zuwa yanzu dai batun ficewar sojopjin Faransa daga kasar ta Nijar shi ne akin kusan dukannin 'yan kasar wanda ake ganin dawowar da wasu kasashe ke yi sannu a hankali domin ci gaba da hulda da kasar ta Nijar tamkar masokiya ce ga shugaban kasar Faransa da ke ci gaba da nacewa a kan bakansa na cewa kasarsa ba ta yarda da sojojin da suka yi juyin mulki ba a matsin halastattaun shugabanin kasar ta Nijar ba.