Faransa na zargin sojin Nijar na garkuwa da jakadanta
September 16, 2023Macron ya ce sojojin da suka hambarar da gwamnatin dimokuradiyya ta Nijar sun toshe duk wasu hanyoyi na kai wa jakadan da abokan aikinsa abinci, lamarin da ya tilasta masa dogara da abincin da sojojin Faransa da ke girke a kasar ke ci.
Karin bayani: Nijar ta umarci yan sanda su fitar da Jakadan Faransa
A karshen watan Ogustan da ya gabata ne dai sabbin jagororin sojan Nijar karkashin Birgediya Janar Abdourahamane Tiani suka bukaci jakadan da ya tattara komatsensa ya fice daga kasar, matakin da Faransa ta ce ba za ta mutumta ba domin sojojin ba halastattun shugabanni ba ne.
Karin bayani: Nijar ta umurci fitar da jakadan Faransa daga kasar
Ministar harkokin wajen Faransar Catherine Colonna ta jaddada cewar jakadan zai ci gaba da zama a Nijar muddin shugaba Macron na kan bakansa, sannan kuma har yanzu hambararren shugaba Mohamed Bazoum shine halastaccen shugaban Nijar.
Karin bayani: Faransa ta ce jakadanta na nan daram a Nijar