Najeriya: Fannin lafiya cikin garari
June 1, 2021Kididdigar baya-bayan nan, ta nunar da cewa kaso 88 cikin 100 na lokitocin Najeriya na tunanin bafrin kasar. Mafi yawansu na tsere wa zuwa kasashen Amirka da Birtaniya, abin da ke kara tabarbarewar fannin kiown lafiyar kasar da dama ke cikin halin tasku. Rashin inshorar lafiya da galibin 'yan Najeriya ke fuskanta ya sa a wasu lokuta kiri-kiri likitoci da ma'aikatan jinya kamar Glory Onyenwe ke daukar dawainiyar kudin magani da aikin da za a yi wa marasa lafiyar domin ceto rayuwarsu.
Karin Bayani:Yajin aikin likitoci cikin annoba a Najeriya
Ma'aikaciyar jinyar Glory Onyenwe ta yi wa tashar DW karin bayani: "Idan har na ce sai na jira an ba ni kudin kafin alkalami kafin na fara duba maras lafiya, to mai nakuda za ta iya mutuwa, za kuma a iya rasa abin da ke a cikinta. Dalilin ke nan da ya sa ba na kwallafa rai a kan kudi, nake kawar da kaina daga abin da zan samu, nake bayar da fifiko a kan yadda zan ceto rayuwar majinyaci.''
A yayin da tashar DW ke tattaunawa da wannan malamar jinya ne dai, wata mai nakuda ta haihu ta hanyar tiyata, to amma kafin a kammala yi mata komai, kwatsam sai aka dauke wutar lantarki. Wannan kuma ya nunawa bako irin kalubalen da ma'aikatan kiwon lafiya ke fuskanta a wurin gudanar da ayyuaknsu. Kazalika irin wannan na daga cikin dalilan da ke sanya wasu likitoci fita zuwa kasashen ketare domin su yi aikinsu cikin kwanciyar hankali. Sai dai bayan wannan dalilin, a cewar Dakta Lumumba Otegbeye wani likita a jihar Legas, akwai likitocin Najeriya ma da albashinsu na watanni ya makale a hannun gwamnati.
Karin Bayani: Dambarwa kan ziyarar Buhari London
Masana dai na cewa idan har Najeriya ta ci gaba da barin likitocin kasar na fantsama kasashen duniya, to za ta ci gaba da tabka asarar kwararru ke nan, a wani abu da ke kama da sakarwa duniya 'ya'yanta masu ilimi da ka iya ceton rayuwar hatta shugabanni na siyasa. Babbar hanyar da masu sharhin ke ganin kasar za ta iya shawo kan matsalar kaurar da likitocin kasar ke yi ita ce, kara kudin da take warewa fannin kiwon lafiya da samar da kayan aiki ga asibitoci.