Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi ganin likita
March 30, 2021Kasa da 'yan sa'oi da baiyana bukatar kai wata ziyara ta ba-zata zuwa birnin Landan, miliyoyin 'yan Najeriya, na cigaba da mayar da martani ga ziyarar Shugaba Buhari da ke gabanin fara wani yajin aikin likitocin da suka shirya gudanarwa a duk fadin kasar. Ziyarar da ke zaman irin ta ta farko cikin tsawon shekaru biyu, a cewar fadar gwamnatin kasar na da ruwa da tsaki da duba lafiya ta shugaban da ya share yinin jiya yana ganawa da jami'ai na gwamnati a Abuja. To sai dai kuma daga dukkan alamu ita kanta sanarwar na shirin barin baya da kura a tsakani na kwararru dama masu adawar kasar da ke mata kallo na gazawa.
Karin Bayani Fargaba dangane da lafiyar Shugaba Buhari
Injiniya Buba Galadima na zaman jigo a jam'iyyar PDP mai adawa a tarrayar Najeriyar da kuma ya ce, shugaban kasar ya share shekaru shida ba tare da ya iya gyara ko da asibitin fadar gwamnatin kasar ba, balle ragowar asibitocin Najeriyar. A baya dai 'yan mulkin tarrayar Najeriyar sun ce za su yi amfani da dubban miliyoyin Nairorin da suka kashe cikin yakin annoba ta coronawajen gyara cibiyoyi na lafiyar kasar. Lamarin da ake ganin ka iya tasiri wajen rage neman magani a kasashen wajen da aka kiyasta na ci wa kasar daruruwan miliyoyi na daloli a shekara. To sai dai kuma daga dukkan alamu annobar Corona na shirin karewa a cikin Najeriyar inda kasar ke shirin komawa cikin karatun lalatattun cibiyoyi na lafiya.
Karin Bayani Najeriya ta kauce wa yin kullen corona don kare tattalin arzikinta
Ita kanta ziyarar shugaban kasar zuwa birnin Landan, na zuwa kasa da kwanaki biyu da fara wani yajin aikin gama gari da zaunannun likitocin tarrayar Najeriyar ke shirin yi a sakamakon gazawa harkoki na lafiya cikin kasar. Tarrayar Najeriyar dai na kashe abun da ya kai kusan dalar Amurka miliyan dubu ashirin wajen neman lafiya ta 'yan boko da shugabanni na kasar da ke tururuwa zuwa kasashen waje, a yayin da kasar ta gaza samar da akalla kaso daya a cikin darin da ake da bukata domin tunkarar harkar ta lafiya mai tasiri.