Martanin janye sojojin Faransa a Mali.
June 11, 2021Fiye da sojojin Faransa dubu biyar ne dai ke jibge a Mali da wasu kasashe makwaftanta, a wani yunkuri na kakkabe 'yan ta'adda da suka mamaye arewacin Mali, kana kuma suna kaddamar da hare-hare har ma a wasu kasashe da ke makwaftaka da ita. Ba zato ba tsammani ne dai Shugaba Emmanuel Macron ya fito fili ya bayyana manufofinsa na soke rundunar Barkhane a Mali da aka kafa a shekarar 2014, bayan ta canji takwararta ta Serval da ta fatattaki 'yan bindiga masu ikrarin kafa daular Muslumci a arewacin Malin. Duk da yake manufofin Macron na nufin sake wani sabon salo game da yaki da 'yan ta'adda, kalaman shugaban dai na ci gaba da janyo ra'ayoyi mabambanta daga masana a kasashen da matsalar ta ta'addaci ta fi shafa tare da yi musu illa da gibi na tattalin arziki kai tsaye.
Karin Bayani: Kokarin shawo kan matsalar tsaro a Nijar
Mouhamadou Sawadogo wani dan kasar Burkina Faso ne, kuma kwararre ta fannin tsaro da ke ganin cewa akwai wuya kasashen da Faransar za ta bari su fitar da kitse daga wuta. A cewarsa janyewar sojojin Faransa a yankin Sahel zai kasance wani babban kalubale ga sojojin yankin musamman ma na G5 Sahel da ke dogaro da karfin wuta da manyan makaman da fasahohin yaki da sojojin ke da shi bayan sun shafe tsawon shekaru fiye da takwas suna yankin. Ya kara da cewa dole ne sojojin a yanzu su dogara da kansu don yakar 'yan ta'adda su kadai duba da yadda suke kara matsa kaimi da hare hare, wanda hakan ke nuni da cewa janye sojojin ya zo a daidai lokacin da ake matukar bukatar kasancewarsu.
Su ma dai 'yan kasar Mali da sojojin kasa da kasa ke yakin ta'addanci ciki har da Faransa, sun nuna rashin fahimtar abin da Macron ke nufi da janye sojojin Barkhane. Riki Kouyaté mamba ne a wasu kungiyoyin fararen hula na Yerewolo. A cewarsa matsalar da Mali ke fuskanta na da alaka da kasancewar sojojin Faransa a kasar. Ko da cikakkun hujjojin Shugaba Macron su ne na soke rundunar Barkhane daga yankin, to amma kuma hakan ba zai hana sojojin Faransar kasancewa a yankin Sahel ba, inda za su ci gaba da aiki kafada da kafada da takwarorinsu na kasa da kasa karkashin jagorancin rundundar nan mai suna Takuba.
Karin Bayani: Shugaban Nijar ya nemi tallafi daga Faransa
To amma a rundunar Takuban ma Faransar ce za ta zama uwa da makarbiya, duk da yake al'ummomi daga ko ina cikin yankin na ci gaba da tsanar zaman sojojin na Faransan. Ko ma dan majaklisar dokoki na jam'iiyyar MPTR mai adawa a Chadi Beral Maikoubou cewa ya yi kasar ta Faransa ma ta san da haka. Kafin wannan matakin ya kammala dai, Barkhane ta kaddamar da hare-hare da dama kan mayakan jihadi a Mali tare da yin gagarumar nasara a kansu. Sai dai duk da hakan tana lamushe makudan kudi daga baitil malin kasar, bayan asarar rayukan sojojinta fiye da 50 da suka kwanta dama sakamakon hare-haren 'yan ta'adda a Sahel.