1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Manyan biranen kasar Spain na fama da karancin haihuwa

October 29, 2024

Rabon Spain ta fuskanci raguwar haihuwa mafi muni tun shekarar 1941. A wasu manyan birane irin su Barcelona, yawan karnuka ya zarta na yara 'yan kasa da shekaru 14, lamarin da ke barazana ga tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/4mM0T
Spain ta kasance kasar da ke da mafi karincin haihuwa a nahiyar Turai
Spain ta kasance kasar da ke da mafi karincin haihuwa a nahiyar TuraiHoto: Cavan Images/imago images

Sannu a hankali, raguwar yawan 'ya'yan da ake haifa a Spain na kara fitowa a fili. Babban misali, shi ne yadda adadin yawan yaran da ake sakawa a makarantu ke ja da baya a duk shekara. Dama wasu alkaluma sun nunar da cewa, an samu raguwar haihuwa a Spain da kashi 24% a cikin shekaru 10 da suka gabata, lamarin wasu da ba sa son haihuwa ke alakantawa da dalilai daban-daban na rayuwa.

 Bruno mai shekaru 33 a duniya, ya ce: " Ko kadan ba na son haihuwa, abokiyar zamana ma haka, baya kuma ga wasu dumbin abokaina. Amma suna kiwon karnuka. Haihuwa idan kana zaune a gidan haya, abu ne da ke zame maka damuwa.''  

Karin bayani:Mata sun magantu kan janye tallafin haihuwa

An bayyana Spain a matsayin kasar da ta fi ko wacce rashin haihuwa a nahiyar Turai. Sai dai, wasu na dora laifi a kan gwamnati saboda karancin tallafin da take bai wa magidanta kamar a sauran kasashe irin su Jamus da Faransa. Hasali ma, wata mace mai suna Ludia ta ce abin takaici a Spain shi ne yadda tsarin gwamnati na dafa wa iyali ke da rauni, alhali kasar na da tsadar rayuwa.


Ludia ta ce: " Dawainiya da yara na da matukar wahala a wannan kasa, kuma ga shi babu wani tallafi na zahiri baya ga watanni hudu kacal na hutun haihuwa. Sannan rayuwa a babban birni, idan kana da yara kuma ba kada dangin Abba balle na Inna, abu ne mai matukar wuya."

'Yan Spain sun zargi gwamnati da rashin tallafa wa magidanta da ke da yawan yara
'Yan Spain sun zargi gwamnati da rashin tallafa wa magidanta da ke da yawan yaraHoto: Richard Zubelzu/picture alliance

Karin bayani:  Tanzaniya: Kula da lafiyar jarirai bakwaini

Amma ga matashiya Isabel mai shekaru 28, lamarin bai takaita a matsalar tallafi ba, domin a nata tunani, wani sa'i dawainiya da yara na hana wa mutun 'yancin sararawa a rayuwarsa ta yau ta kullum. Ta ce: " Renon ciki abu ne da ke daukar lokaci mai tsawo, ni matashiya ce ina da abubuwa da dama da suke gabana a madadin kula da jariri. Sannan kuma bana son yara dayawa a don haka ba na tunanin zan iya kula da jiriri.''

Karin bayaMatsalar rashin haihuwa a jinsin mazani: 

'yan Spain sun fi ba wa karnuka muhimmanci fiye da yawan haihuwa
'yan Spain sun fi ba wa karnuka muhimmanci fiye da yawan haihuwaHoto: Far from Fear eV

Yayin da makarantu ke rufewa saboda karancin yara a Barcelona, wani bincike ya nunar da cewa, adadin yawan karnuka ya zarta na yara 'yan kasa da shekaru 14 a birnin, lamarin da ke tayar da hankalin mutane da dama ciki har da Lolanda Abad, daraktar wata makaranta da ke cewa: " Birnin da ba yad a yara, sunansa matacen birni. Za ku iya tunanin birnin da babu dariyar yara? Idan ba mu karfafa yawan haihuwa ba, ban san yadda makomarmu za ta kasance a nan gaba ba.''

Babbar damuwa da wannan matsala ta rashin haihuwa ra haifar a Spain ita ce ta rashin wadanda za su canji ma'aikatan da ke ritaya, wannan dalili ne ya kai firaministan kasar Pedro Sanchez ga karfafa gwiwa ga shige da ficen 'yan ci rani domin cike wannan gibi.