Najeriya: Martani kan shirin zaben 2023
October 16, 2020Sanar da ranar da za a yi zaben shugaban kasa a Najeriyar, na nuna sake kada kugen siyasa a kasar da tuni ake ta hasashe da zarya a tsakanin 'yan takara. Wannan ne dai karo na farko da hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da ranar da za a yi zaben shugaban kasa a Najeriyar fiye da shekaru biyu kafin lokacin, abin da ake wa kallon ko dai kokari ne na fara shiri da wuri domin guje wa makara ko kuma wani sabon salo ne.
Karin Bayani: Buhari ya bukaci hadin kan 'yan Najeriya
Hukumar zaben Najeriyar dai ta tsara tare da alkawarin cewa, a zaben kasar na shekara ta 2023, za ta yi amfani ne da naurar computer. Tuni 'yan siyasa suka fara mayar da martani kan matakin. Sai dai ga Lawali Ibrahim Dan Galadiman Zurmi wani dan siyasa da ke bibiyar al'ammura, ya ce abin da ya dame su a yanzu, ba batun ranar zabe ba ne.
Karin Bayani: Kallo ya koma zaben gwamnoni a Najeriya
Tuni dai ake nuna adawa da daya daga cikin mutanen da shugaban Najeriyar ya tura majalisa wato Lauretta Onoche wacce ita ce mai taimakawa ta musamman ga shugaban Najeriyar, amma kuma yake son a nadata a matsayin kwamishiniya a Hukumar zaben kasar INEC, matakin da tuni jam'iyyar adawa ta PDP ta nuna kin amincewarta da shi. Zaben shugaban kasa a Najeriya dai shi ne yafi daukar hankali a tsakanin al'umma, saboda karfin iko na tsarin da ake amfani da shi a kasar.