Zaben 2023: Makomar adawa a Najeriya
July 1, 2021Akalla gwamnoni uku ne dai ko bayan 'yan majalisun dattawa da wakilai a tarayya da jihohi, suka fice daga jami'iyyar PDP ta adawa ya zuwa APC 'yar mulki a Najeriyar daga bangare dabam-dabam cikin kasar. Duk da cewar dai kusan ya zama al'ada, sauyin shekar a tsakanin jam'iyyun kasar a lokutan da ake fuskantar zabe, komawar kimanin gwamnoni biyu cikin tsawon kasa da watanni biyu dai, na daukar hankali a kasar da ke kallon barazana mai girma.
Karin Bayani: Jam'iyyar APC ta ce ba ta damu da fitar Saraki ba
Akwai dai tsoron babakeren jam'iyya guda daya, na iya sauya makomar dimukuradiyya a Najeriyar da kila kama hanyar yin kama karyar ga 'yan kasar. Alhaji Tanko Yakasai dai ya share lokaci yana taka rawa cikin siyasar Najeriyar da kuma ya ce kokarin kashe gasa a siyasar na barazana har ga makoma ta kasar a nan gaba. Ridda cikin siyasar Najeriya ko kuma shan koko mai kama da daukan rai dai, sauyin shekar kuma a tunanin Injiniya Buba Galadima da ya share lokaci yana sana'ar ta adawa, na zaman alamun kasawa a bangaren PDP da a cewarsa har yanzu ke karatun tatata a adawar.
Halin da ke kama da zannen dutse, ko kuma gwagwarmaya ta neman mafita a shekarun da ke tafe dai, ana kallon rage karfin na adawa na iya shafar kokarin 'yan lemar na karbe mulki daga APC ta masu tsintsiya. To sai dai kuma a tunanin Sanata Umar Tsauri da ke zaman sakataren PDP na kasa, masu sauyin shekar na zaman azzaluman da ba su iya jure zama a tsarin na adawa.
Karin Bayani: Rikici na kara mamaye siyasar Najeriya
Koma ya take shirin kayawar a makomar ta adawa dai, ga Faruk BB Faruk da ke zaman kwararre a siyasar Tarayyar Najeriyar, rashin akida tsararra ne ya sanya sauyin shekar ke kama da sauyin riga a siyasar kasar a halin yanzu. Ana dai kallon yiwuwar sake tashin sabuwar jam'iyyar ta adawa, ga da dama a cikin 'ya'yan jam'iyyun biyu da ke kusantar zaben shekara ta 2023, ba tare da matabbata ta makoma mai kyau ba.