Halin kunci yayin bukukuwan Sallah
May 2, 2022Yayin da ake ci gaba da gudanar da bukukuwan karamar Sallah a fadin duniya baki daya bayan da al'ummar Musulmi suka kammala azumin watan Ramadana, a jihar Kano kamar sauran jihohin Najeriya an yi Sallar Idin na bana lafiya. Duk da kuncin rayuwa da ake fama da shi a Najeriyar dai, al'umma sun kasance cikin farin ciki yayin shagulgulan Sallar ta yadda mutane suka nuna ahalin taimakawa juna musamman bayar da tallafi ga marasa karfi. Koda yake wasu sun yi Sallar ba tare da kudi a hannunsu ba, musamman ma 'yan fansho a jihar ta Kano da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya. Ba dai matsalar tattalin arziki da ya haddasa halin kunci a tsakanin al'ummar Najeriyar ne kadai ke addabar kasar ba har ma da batun rashin tsaro, inda ake sace mutane domin neman kudin fansa a yankin Arewa maso Yammaci da kuma Tsakiyar kasar. A hannu guda kuma yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar musamman jihohin Borno da Yobe, har kawo yanzu suna fama da matsalar hare-haren 'yan ta'adfdan Boko Harama da ke gwagwarmaya da makamai. Matsalar rashin tsaro a Najeriyar dai, ta haddasa asarar rayukan dubban mutane tare da sanya firgici a zukatan al'umma.