Makamai sun yi batan dabo a Najeriya
January 3, 2022A baya dai duk wani batu game da hanyoyin shigar makamai a cikin Najeriyar, na karkata ne ya zuwa kasar Libya da ke zaman cibiyar daukacin makaman da ke yankin Sahel. To sai dai kuma wanna sabon rahoton da ya ambato batan bindigogi kimanin dubu 88 dai, ya bi diddigin yadda makaman suka rika bata a makarantu da cibiyoyin horaswa da ofisoshin 'yan sanda na jihohi da gunduma. Duk da cewar dai rahoton bai ambaci makomar dimbin makaman masu tayar da hankali cikin Tarayyar Najeriyar da ke cikin rikicin rashin tsaro ba, akwai dai tsoron mafi yawan makaman na iya karewa a hannun barayin daji da ragowar masu tayar da hankalin kasar a halin yanzu.
Karin Bayani: Najeriya za ta hukunta dillalan haramtattun makamai
Tuni dai da ma aka rika fidda rahotannin barin makamai a bangaren sojan Najeriya da ke yakar Boko Haram, kafin sabon rahoton da ke fito da yadda kasar ke kara shiga rudu a kokarin kai karshen matsalar rashin tsaron fili. To sai dai koma ina kawancen da ke tsakanin gurbatatattun jami'an tsaron da barayin ke iya kai wa a kokari na kara kwarara ta jini a cikin Najeriyar dai, sabon rahoton na kara nuna irin jan aikin da ke gaban 'yan mulkin masu kisan kudi a shekara domin karin karfi ga jami'an tsaron kasar.
Sai dai a fadar Aliyu Alhassan da ke zaman tsohon mukaddashin kwamishinan 'yan sanda a Najeriyar, jami'an 'yan sandan na zaman na kan gaba wajen fuskantar barazanar kai hari da karbe makamai cikin kasar a halin yanzu. Bara gurbi tsakanin 'yan sanda ko kuma farauta ta masu kokarin kare rayuwar al'umma, sabon rahoton na shirin bude idanun 'yan mulkin da ke tsakiyar aikin kara yawan jami'an 'yan sanda a kasar.
Karin Bayani: Mallakar bindiga domin kare kai a Najeriya
A bana kadai dai rundunar ta yi nasarar daukar sababbin 'yan sanda dubu 10, domin cike gibin jami'an tsaro a Najeriyar. Kuma a fadar Yahuza Getso da ke sharhi kan batun tsaron, sabon rahoton na kara fitowa fili da irin tasirin daukar baragurbi cikin hukumar 'yan sandan da ke da jan aikin bayar da kariya ga dukiya da rayukan al'umma a kasar. Ta dai kai ga daya a cikin gwamnonin yankin Arewa maso Yammacin kasar, umartar daukar makamai da nufin kare kai sakamakon rashin tsaron da ke neman ya wuce da sanin 'yan mulki.