Najeriya: Martani kan maida hukumomi zuwa Legas
January 19, 2024
Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ACF na nazarin sabon matakin da ke iya tasiri ga rayuwa da makomar al'ummar yankin. A cikin salo na neman sauki ne dai Abujar ta fara Shirin kwashe ma‘akatun da hukumomin dake da tasiri ciki na tattali na arzikin kasar zuwa birnin Ikkon.
Akalla bangarori guda biyar da ke cikin babban bankin kasa CBN ne dai aka tsara zasu koma Ikko. A wani abun da ke iya shafar ma‘aikata da dama da ke yiwa bankin aiki.
Majiyoyi a cikin bankin dai sun ce ana samun karuwar matan aure da ke tunanin ajiye aiki, da nufin kauce wa zuwa Ikkon da ke iya kaiwa ga rabasu da iyali.
Karin Bayani: Kokarin mayar da hukumomin gwamnati daga Abuja zuwa Legas
Koma wane tasiri shirin komawa ikkon ke iya yi ga rayuwa da makomar cikin kasar an sha kallon yunkurin mayar da hukumomin zuwa Ikko a bangaren shugabbanin kasar da ke da cibiyarsu a yankin Kudu maso yamma.
Tsohon shugaban Najeriya Obasanjo ne dai alal misali ya dauke ofisoshin hukumomin tashoshin jiragen ruwa da ma ruwayen tarrayar Najeriyar daga birnin na Abuja zuwa Ikko, kafin sabon yunkurin a bangaren sabuwar gwamnatin tarrayar Najeriyar.
Abun jira a gani dai na zaman tasirin shirin a bangaren gwamnatin kasar da ke kan mulki da al'ummar arewacin tarrayar Najeriyar da ke tunanin dora masu tsintsiyar bisa mulkin kasa.