Matasa na zanga-zanga a Najeriya
October 15, 2020Tun dai a makon jiya ne wasu matasa a Tarayyar Najeriyar, suka fara gudanar da zanga-zanga a manyan birane biyu na kasar wato babban birnin kasar Abuja da kuma cibiyar kasuwancin kasar Lagos. Suna dai yin zanga-zangar ne da nufin tilasta rusa rundunar 'yan sandan musamman da ke yaki da fashi da makamai a kasar wato SARS.
Sai dai kuma, ko bayan da babban sfeto janar na 'yan sandan kasar Mohammed Adamu ya sanatr da rusa rundunar ta SARS da kuma maye gurbinta da rundunar SWAT, matasan ba su fasa zanga-zangar ba, inda suka ce baki dayan rundunar 'yan sandan suke da bukatar a yi wa kwaskwarima, da ma wasua bukatunsu da suke so a biya musu.
Su ma dai matasan yankin arewacin kasar sun dauki matakin yin zanga-zangar, a daukacin jihohin Arewa, inda su kuma ke bukatar lallai sai gwamnati ta magance matsalar rashin tsaro da rashin ci-gaba da ke addabar yankin.