1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zanga-zanga a jihohin Arewa

October 15, 2020

Matasa da malaman addinai tare da mawaka da masu shirya fina-finai da kungiyoyin mata daga jihohin arewacin Najeriya, sun gudanar da zanga-zangar lumana da ta banbamta da wadda takwarorinsu na kudancin kasar suka yi.

https://p.dw.com/p/3jyrG
Zanga-zanga na daukar sabon salo a Najeriya

Wasu masana tsaro dai na ganin cewa kamata ya yi matasan kasar su hada kai gabaki daya domin tunkarar kalubalen da ke damunsu, maimakon kowane yanki ya shirya tasa zanga-zangar. Daruruwan matasa da malaman addinai da mawaka da kungiyoyin matan daga daukacin jihohin arewacin Najeriyar, sun bayyana cewa sun fito zanga-zangar ne sakamkon tabarbarewar tsaro da rashin kwanciyar hankali, tare da yadda garkuwa da satar jama'a ya zamo ruwan dare.

Karin Bayani: Sukar rundunar 'yan sandan SWAT a Najeriya

Tattakin wanda aka fara shi tun da safiyar yau da misalin karfe takwas da rabi na safiya, an ga mata da kananan yara dauke da kwaleye masu rubuce-rubuce dabam- dabam a kan tituna, inda suke jaddada bukatar da ke akwai wajen daukar kwararan matakan yaki da 'yan ta'adda na Boko Haram da masu sace mutane.

Kwamared Sa'adu Bako shi ne jagoran shirya gangamin a jihar Kaduna, ya nunar da cewa wannan yankin na kowa da kowa ne wuraren sakamkon fama da ake da matsalar tsaro da zubar da jini a yankin arewacin Najeriyar, inda ya ce akwai bukatar inganta tsaro wanda rashinsa ke janyo koma baya a bangaren tattalin arziki da Ilimi da sauran harkokin da suka jibanci na ci-gaban kasa da alumma, maimakon soke rundunar tsaron SARS a kasar baki daya.

Karin Bayani: Murna bayan rusa rundunar SARS

Zanga-zangar da matasan kudancin kasar suka gudanar a kan bukatar kawo karshen ayyukan rundunar tsaro ta SARS da ke yaki da 'yan fashi da  makami, ta zaburar da al'ummar arewacin Najeriyar. Cikin masu yin wannan tattaki dai, har da manyan malaman addinai da suka hadar da Pastor Yohanna YD Buru, wanda ya ce yankin Arewa ya fi kowanne fadawa cikin matsalar tabarbarewar tsaro, inda ya ce  wannan dalilin neya sanya su yin kira ga gwamnatin Najeriyar da ta yi duk mai yiwuwa, wajen ceto daukacin al'ummar yankin daga kalubalen da suka fada na tabarbarewar tsaron. Acewar wani dattijo Musa Danladi abun takaici ne yadda sata da garkuwa da mutane, ke naman zama wata sabuwar sana'a a daukacin arewacin Najeriyar, lamarin da ke bukatar daukar matakan gaggawa domin magance shi.