Rikicin siyasar jihar Rivers ya dauki sabon salo
December 12, 2023Tun dai bayan sauya shekar da 'yan majalisa 27 da ke goyon bayan tsohon gwamna don bijire wa gwamna Siminalayi Fubara, gaggan 'yan siyasar jihar da sauran masu ruwa da tsakin ke ta ruguguwar daukar bangare, walau na tsohon gwamna Nyesom Wike ko kuma na gwamna mai ci Siminalayi Fubara.
Karin Bayani: Rigimar 'yan siyasar jihar Rivers ta munana
Ko dayake wasu masu lura da al'amura, na ganin rigimar siyasar ta Rivers ba abu ne da zai haifar da alkhairi ga jihar ba.
Wata babbar kotu a jihar, ta yanke hukuncin tabbatar da Hon Ehie Edison wanda mai goya wa gwamnan baya ne, a matsayin halastaccen shugaban Majalisar dokokin jihar sannan ta ja kunnen Hon Martn Amaewhule daga nuna kansa a matsayin shugaban majalisar.
Tuni dai Gwamna Fubara ya yi wani zaman tattaunawa kan kasafin kudin shekarar 2024 a fadar gwamnati, da ya kai Naira biliyan 800, da kuma ke gab da kai wa majalisar jihar don samun sahalewarta.
A halin yanzu dai za a iya cewa duba da shekaru takwas da Wike ya yi, kuma yanzu yana Ministan babban birnin tarayya Abuja, suka sa ake ganin lamarin zai fi karfin Fubara duk da karfin da gwamnoni suke da shi.