Martanin Najeriya kan gargadin Amurka
November 7, 2023Jan hankali da kuma gargadin yin taka tsan-tsan da kasar Amurkan ta yi ga masu ziyara da gudanar da harkokinsu a Najeriya musamman ‘yan kasarta, wanda ofishin jakadancin Amurkan da ke Najeriya ya ce yana da sahihan bayanai da suka tabbatar da barazanar a kan otel otel a manyan biranen Najeriyar. Wannan dai kara daga batun ne da ma bashi karfi bisa ga wanda Amurikan ta yi a baya a cewar Dr Kabiru Adamu shugaban cibiyar Beacon da ke aiki a fanin tsaro a Najeriyar.
A baya dai barazana irin wannan ta tada kura sosai a Najeriya, inda ra'ayoyi kan sha bamban a kan yadda Amurkan ke fitar da irin wannan gargadi kan barazanar da take dangantawa da rashin tsaro. Da alamu a wannan karon abin ya taba gwamnatin Najeriyar da ta kai ga mayar da martani a kan illar da take gani kan wannan sanarwa kamar yadda ministan yada labaran Najeriya Alhaji Mohammed Idris ya nunar.
A kwanakin baya hukumomin tsaron Najeriya sun bankado yunkurin kai hare-hare a biranen Minna da ke jihar Niger da birnin Kano inda ta kama makamai masu yawa, baya ga nasarar murkushe ‘yan ta'addar. Sai dai an fuskanci wasu munana hare-hare a Maiduguri da Katsina.
Ra'ayoyi dai sun shan bamban a kan irin wannan gargadi da Amurikan kan fitar na barazanar ta tsaro.