Gwamnatin Najeriya ta kai karar likitoci
August 17, 2021Fuskantar kiki-kaka a tsakanin gwamnatin Najeriyar ne dai, ya sanya gwamnatin neman kotu ta shiga tsakani domin raba gardama tsakaninta da likitocin da suka tirje kan cewa ba ta cika alkawarin da tai musu ba yayin da gwamnatin ke musanta hakan. Tunkrar kotun dai wani sabon salo ne wai kaza ta ji ana shika da dare, domin gwamnatin ta saba gayyatar ma'aikatan da suka daka yajin suka sha domin sulhuntawa a kuma rarrashi a ba su hakuri. Sai dai na kasa cimma matsaya bayan tattaunawa ne gwamnatin Najeriyar ke tunkarar kotun domin raba gardama, amma raba gardama a kan yajin aikin da ya shafi harkar lafiya babban al'amari ne.
Ma'aikatar kwadago da inagantuwar aiki ce dai ta bayyana shigar da karar da har an yi zaman farko a kotu. Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da anobar kwallara ke ci gaba da barna a Najeriyar, inda cibiyar kula da kare yaduwar cututtuka ta Najeriyar ta bayyana cewa ta halaka mutane 1,374. Da alamu dai wannan yajin aikin zai dauki lokaci mai tsawo ana gogawa in dai ba an samu wani sauyi daga bangaren gwamnatin ba, domin zaman farko na shari'ar an dage shi zuwa ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa.