1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Najeriya cikin matsin rayuwa

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 10, 2020

Al'ummar Najeriya sun samu kansu cikin halin taskun rayuwa, tun bayan da mahukuntan kasar suka kara kudin wuta da farashin man fetur, abin da ya haddasa tsadar kayan masarufi da ma uwa uba kayan abinci.

https://p.dw.com/p/3iHLe
Cartoon Preisanstieg in Nigeria
Tsadar kayan abinci da na masarufi na takura rayuwa a Najeriya

An dai jima ana cikin halin tasku na matsin rayuwa a Tarayyar Najeriya, kwatsam sai duniya ta tsinci kanata cikin halin annobar coronavirus. Tattalin arzikin duniya baki daya dai, ya shiga cikin rudani, sakamakon dokar kulle ko kuma hana zirga-zirga da zaman gida dirshan da aka sanya a kasashen duniyar domin dakile yaduwar wannan annoba, abin kuma da ya tsayar da harkokin kasuwanci cak.

Najeriya ma dai ba a barta a baya ba wajen sanya irin wannan doka da kuma tsayar da harkokin kasuwanci, abin da ya janyo karancin kudin shiga ga kasasr da ma talakawanta kasancewar mafiya yawan al'ummar kasar sai sun fita sannan su samo abin da za su saka a bakinsu na salati.

Sai dai kuma al'ummar Najeriyar ba su gama fita daga wannan halin matsin ba bayan da aka dan sassauta dokar kullen a duniya ciki kuwa har Najeriyar, sai gwamnati ta bayyana karin farashin mai da kuma kudin hasken wutar lantarki, adaidai lokacin da farashin kayan masarufi da ma uwa uba kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi. Hakan dai ya kara jefa talakawan wannan kasa cikin halin taskun rayuwa.