Kaddamar da sabon kudiri a Najeriya
September 9, 2020Wannan dai ya biyo bayan karewar shirin dora Tarayyar Najeriya cikin kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya na Vision 2020 ba tare da kai wa ga biyan bukata ba. Kama daga vision 2010 ya zuwa ga 20- 20-20, ya dai zamo salo a tsakanin 'yan mulkin Najeriyar na tsara tattalin arzikin kasar ba tare da kai wa ya zuwa cika burin miliyoyi na 'yan kasar da ke halin kunci ba.
Karin Bayani: Barazanar karancin abinci a Najeriya
Kasar ta share shekaru kusan 60 a cikiin 'yanci tana kwan gaba kwan baya, a kokari na neman mafita ya zuwa tudun mun tsira kan batun tattalin arzikin. A bana dai kimanin tsare- tsare guda biyu na tattalin arzikin ne ke shirin kai karshe ba tare da cimma burin kasar na zamowa a cikin kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniyar ba.
Tattalin arzikin Najeriya na cikin rudu
Sai dai kuma a karon farko Najeriyar na shirin sauyin taku tare da kaddamar da wani sabon shirin da ke da burin ceton mutane miliyan 100 a kasar daga hali na talauci a shekaru 10 da ke tafe.
Agenda 2050 da ke zuwa kasa da 'yan watanni da kaddamar da tsarin ciniki na bai daya a tsakanin kasashe na nahiyar Afirka dai, na zaman sabon fata ga kasar na goga kafada a duniyar da kaucewa dogaro da hajar man fetur ga rayuwar al'umma. Zainab Shamsuna Ahmed dai na zaman ministar kudin kasar kuma daya a cikin jagororin shirin guda biyu da kasar ta dorawa alhakin zuwa tudun mun tsira ko da rarrafe ko da gudu.
Karin Bayani: Zanga-zangar adawa da wahalar rayuwa a Najeriya
Duk da jerin tsare-tsare, a baya dai Najeriyar na ji a jiki daga faduwar farashin man fetur da annobar COVID-19 da ke barazana ga makoma ta 'yan kasar. Ana dai shirin kaddamar da sabon shirin ne, a daidai lokacin da daukacin kasar ke cikin rudani sakamakon rashin kudi a bangaren mahukunta da kuma zare tallafin makamashi da karin farashi da suka haifar da tsadar rayuwa a bangaren talakawa. Nan da shekaru 30 da ke tafe dai, Najeriyar ce za ta kasance kasa ta hudu a duniya mafi yawan al'ummar da aka kiyasta za su kai miliyan 400.