Rage amfani da makamashin da ba a sabuntawa
December 13, 2023Bayan gomman shekaru ana tattaunawa, kasashen duniya sun cimma gagarumar yarjejeniya inda suka yi kiran janyewa sannu a hankali daga amfani da makamashin da ba a sabuntawa, ko da yake taron bai yanke karara cewa za a daina amfani da makamashin wanda ya hada da kwal da man fetur da kuma gas ba.
Karin Bayani: Dubai: Yunkurin kasashen duniya na rage dumamar yanayi
Kasar Hadaddiyar daular Larabawa wadda ta karbi bakuncin taron ita ce ta gabatar da kundin yarjejeniyar wanda kasashe kimanin 200 da suka halarci taron suka amince.
Masana kimiyya sun yi ammanar cewa makamashin kwal da fetur da kuma gas suna taimakawa wajen fidda gurbatacciyar iska ko hayaki da ke gurbata muhalli.
Wannan dai shi ne karon farko da aka cimma irin wannan yarjejeniya cikin shekaru da dama a tarihin tarukan muhalli na Majalisar Dinkin Duniya.
Masana dai na ganin har yanzu da sauran rina a kaba wajen cimma kudirin kare dumamar duniya da kuma illar da hakan ke haifarwa a cewar Dr Auwal Faruk Abdulsalam shugaban tsangayar nazarin Muhalli ta jami'ar jahar Kaduna a Najeriya.