Ghana: Kishi,na saka rayuwar iyali cikin hadari
May 2, 2024Zeinab Mohammad Ali,uwar yaya biyu ta fada wa kotu cewa ta aikata laifin ne a yunkurin kare kanta. Sai dai kuma bayanan ba su gamsar da alkalin kotun ba, wanda ya zartas da hukuncin. Irin wannan al'amari daya ne daga cikin misalai a Ghana inda bayan samun tashin hankali sautari saboda kishi mata kan dauki mataki a kan mazajensu ta hanyar jikkatasu.
Kishi dalilin samun yawan rikici a tsakanin ma'aurata a Ghana
Yanzu haka dai mijin wannan mata yana kwance a asibiti yana yin jinya babbar ayyar tambaya ita ce ko wanne dalili ne ke janyo kiyayya tsakanin ma'aurata a Ghana. Malama Mannara Abdulmumuni, mai ba da shawarwarin aure a gidauniyar nan ta Peace da’awa ta ce yawanci kishi ne na matan kan yawan janyo tashin hankalin da zaran miji ya bayyana aniyarsa na yin karin aure.