Najeriya: Kasafin kudin kasar na shekara ta 2024
November 28, 2023Ya zuwa yanzun dai sama da kaso 80 da doriya na kudade na shigar tarrayar Najeriya dai na tafiya ne ga biyan kudin ruwa dama bashin dake ta kokarin rinjaya ga kasar. A yayin kuma da ragowar 20 din ke tafiya ga kokari na inganta rayuwar al'umma. Sama da Naira Triliyan Biyu da Rabi ne dai alal ga misali kasar ta batar a wattani shida na farko na shekarar bana, cikin neman sauki nauyin dake ta nuna alamu na karuwa cikin kasar a halin yanzu.
Kasafin triliyan 27.5 na shekara mai zuwa ta 2024
To sai dai kuma gwamnatin tarrayar Najeriyar ta ce tana da isassu na kudade na batarwa a kokari na sauke nauyi na yan kasar a shekarar badi. Atiku Bagudu dai na zaman ministan kasafin kudin kasar kuma yace gwamnatin tinubun tana da karfin sauke nauyi d akila alkawuran zaben da ke tsakaninta da al'umma ta kasar. Bola Ahmed Tinubu zai isa majalisar dokokin nan gaba da nufin mika kasafin kudin kasar irinsa na farko ga sabuwar gwamnatin. Kasafin na triliyan 27.5 dai na zaman mafi girma cikin tarihi na kasar da ke da dimbin bashin daya kai trilliyan 87 a halin yanzu.
Bashi ya yi wa Najeriya katutu ga kuma karancin kudaden shiga
Rashin kudin shigar dai da dimbin bashin dai ya yi nisa wajen dada ruda masu mulki na Abujar da ke fadin ta yi baki ga tattali na arziki cikin kasar. Dr Hamisu Ya'u dai na zaman kwarrare ga tattali na arzikin Najeriyar, kuma ya ce da kamar wuya sauke nauyin a bangare na gwamnatin da ke dada tunkarar bashi da nufin biya na tsohon bashin a bangare na masu mulki na kasar. Bashin da ke shirin komawa hanji, ko kuma so na zuciya cikin halin mulki, a cikin kasa da tsawon wattanni guda shida dai sabuwa ta gwamnatin ta karbo karin bashin da ya kai dalar Amurka miliyan Dubu Biyu. Kuma a yayin da Abujar ke kara zare tallafi babu alamun ragin kisan kudin tafi da gwamnati, da a cewar faruk BB faruk ke zaman bukatar ingantar rayuwar al'umma.
‘