Olaf Scholz: Dan hakin da ka raina
December 8, 2021Kwatsam Olaf Scholz ya tsaya a matsayin dan takarar jam'iyyar SPD a zaben 202, abin kuma da ya kai shi ga nasara a zabe. Shin wane ne dan siyasar da ya farfado da jam'iyyar SPD da ta karbe mulki daga jam'iyyar CDU da abokiyar tagwaitakarta CSU ta Angela Merkel na tsawon shekaru 16? A daren ranar zaben Jamus na watan Satumbar da ya gabata, Olaf Scholz ya dare mumbari a shalkwatar jam'iyyarsa ta SPD, inda magoya bayansa suka kece da sowa da tafi na yabo da jinjina. Scholz ya cimma wasu nasarori da suka sanya jam'iyyar ta masu sassaucin ra'ayi a zukatan Jamusawa, sakamakon jajircewa da bajintar da ya nuna a baya-bayan nan.
Karin Bayani: Kafa gwamnatin hadaka a Jamus
Bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayyana shirinsa na aiwatar da sauye-sauyen da za su canza salon siyasar Jamus, duk da cewa ya sha alwashin bin salon mulkin Angela Merkel da ya gada. Ya ci gaba da kare manufofin sabuwar gwamnatin da zai jagoranta, yayin muhawara a kafafen talabijin da hirarraki da kafafen yada labarai gabanin zaben. A tsawon wannan lokacin, jam'iyyarsa ta SPD na biye da shi sau da kafa. Shugabanci dai ba sabon abu ba ne ga Scholz domin ya taba rike mukamai, kama daga na ministan kudin Jamus da kuma mataimakin shugaban gwamnati a gwamnatin hadaka ta CDU/CSU da kuma SPD lokacin da ake danganta shi da mai tsauttsauran ra'ayi a cikin jam'iyyarsa mai matsakaicin ra'ayi.
Daga karshe ya zama mutumin da jam'iyyar ta yanke shawarar tsayarwa a matsayin dan takararta, a zaben da ya gabata. Ga Scholz a lokacin ne suka kulla kyakyawar dangantaka cikin amana da 'ya'yan jam'iyyarsa ta SPD da za a ce ta kai su ga gaci, kamar yadda ya kara tabbatarwa bayan da jam'iyyar ta lashe zaben da 'yar karamar tazara: "Mun hada kai a matsayin jam'iyya guda, mun rike juna tare da nanata wa junanmu nasarar da muke son cimma, kuma mun yi nasarar lashe zaben Jamus.''
Karin Bayani: Rikici bayan zaben 'yan majalisar dokokin Jamus
Baya ga rike mukamai kamar ministan harkokin cikin gidan Jamus da na magajin garin Hamburg jiharsa ta asali da ake ganin sun taimaka a gogewar da ya samu a siyasance, Scholz gogaggen dan kasuwa ne da ya yi alkawarin yaki da sauyin yanayi. Ya daura damarar ceto kasar daga barazanar dumamar yanayi, guda daga cikin manufofin gwamnatin hadakar da zai jagoranta: ''Nauyin kasar baki daya, ya rataya a wuyanmu. Yanzu ba ta tamu muke ba, damuwarmu al'ummar kasarmu da aikin da ke gabanmu na kare muhalli daga barazanar sauyin yanayi da wanda dan Adam ya haddasawa kansa, shi ne burin da ke gabanmu''
A cikin shekarun da ya shafe a fagen siyasar Jamus ya gamu da tarin matsaloli, duk da haka ba su sa shi kaucewa alkiblar da ya sa a gaba ba har zuwa lokacin da annobar corona ta barke. Scholz a matsayinsa na ministan kudi, ya taka muhinmiyar rawa domin ganin kasar ta dakile cutar. Ko bayan lashe zaben da kafa gwamnatin hadakar, ya ce tsugune ba ta kare ba a yaki da annobar da ke kokarin haddasa rabuwar kawuna a tsakanin 'yan kasa. Yanzu dai an zura idanu aga yadda za ta kaya a takun Olaf Scholz da majalisar ministocinsa da ta kunshi ministoci 16 bakwai daga jam'iyyar SPD, biyar daga jam'iyyar The Greens, hudu kuma daga jam'iyyar FDP a majalisar dokoki ta Bundestag.