Tunusiya: Shekaru 11 da guguwar sauyi
December 17, 2021Dubu-dubatar al'ummar Tunusiya sun yi cikar kwari kan titunan birnin Tunis fadar gwamnatin kasar, bayan sallar Jumma'a albarkacin tunawa da ranar 19 ga watan Disamba na shekara ta 2010 da ke zama ranar da matashin nan mai suna Mohamed Bouazizi ya cinnawa kansa wuta domin nuna takaicinsa ga kwace amalanken da yake tallan kayan marmari da wata 'yar sanda ta yi. Wannan lamari dai, ya zamo sanadiyyar barkewar zanga-zangar da ta rikide zuwa juyin-juya hali a kasar tare da bazuwa a kusan galibin kasashen Larabawa. A wancan karon dai bukatun tattalin arziki da kawo karshen mulkin mutu ka raba na marigayi tsohon shugaban kasar Zine el-Abidine Ben Ali ke zama jigon bazuwar mutane kan tituna domin neman sauyi.
Sai dai kuma a wannan karon bayan wadancan bukatu matakan da shugaban kasar Kais Saied ya dauka na tattarawa kansa iko da sauya kundin tsarin mulki bayan rusa majalisa da shirin gudanar da zaben 'yan majalisu nan da shekara guda da ya yi ne suka kara tunzura al'umma yin zanga-zangar neman sauyin. Shugaban majalisar da aka rusa Rached al-Ghannouchi na jam'iyyar Ennahda mai ra'ayin Islama, cewa ya yi babu wanda zai lamunci batun sake zaben 'yan majalisu da kwaskwarima ga kundin tsarin mulki domin bukatar wasu daidaikun da suke son rufe rashin iya mulkinsu. To sai dai a hannu guda, magoya bayan Shugaba Saied din suma sun shirya tasu zanga-zangar goyan baya ga gwanin nasu. A cewarsu matakan da yake dauka ne za su kai ga cimma burin juyin-juya halin da aka yi shekaru 11 da suka gabata da ya gaza tsinanawa 'yan kasar komai, saboda mummunan tsarin siyasar da ake bi a kasar.