Injin da zai tattara sakamakon zabe
September 28, 2021A wani abun da ke kama da fatalwar zabe a Najeriya, gamin gambiza ta kungiyoyin fararen hula sun ce ya zama wajibi amfani da injinu masu kwakwalwa wajen aikawa da sakamakon zabe daga rumfunan zabe a zabukan 2023 da ke tafe. Ya zuwa wannan Talata, majalisun tarrayar Najeriyar guda biyu, sun kafa kwamitin nazarin sabuwar dokar da ke shirin jagorantar zabukan kasar da ke tafe.
Karin Bayani: Najeriya: Rikicin siyasa da zaben 2023
To sai dai kuma ana cigaba da musayar yawu a tsakanin sasssa dabam- dabam da ke neman sauyin fasalin tsarin zaben da mai da shi na zamani. Kuma na kan gaba dai na zaman kungiyoyi na fararen hular da ke sanya ido a zabukan kasar da kuma ke fadin ya zama wajibi komawa ga zamani domin kai wa ya zuwa ingantattcen zabe cikin kasar.
Misali, ya zama wajibi a fara ta kungiyoyin aika sakamakon zaben ta injinu masu kwakwalwa daga rumfunan yin zaben ya zuwa cibiyoyi na hukumar zaben domin tarasu. Auwal Musa Rafsanjani dai na zaman jigo a kungiyoyin da ke sa ido a harkar zabe cikin kasar da kuma ya ce, aikawa da zaben ta injuna masu kwakwalwa na zaman hanyar kaucewa magudin zabe a kasar.
Karin Bayani: Gardama kan gyaran dokar zabe
Da dama na 'yan majalisun kasar biyu, sun sa kafa suka, sun shure tunanin amfani da zamanin a zabukan tarrayar Najeriyar da ke tafe a shekarar 2023. Kafin sake dago hakarkarin da ke zuwa a daidai lokacin da wasu kwamitocin majalisun kasar guda biyu ke yanke hukuncin karshe a kan batun.
Kutse a cikin zabe ko kuma kokari na tadda zamani, zai dauki shekaru kusan 10 da doriya kafin iya kai wa ya zuwa ga amincewa bisa sabuwar dokar zabe ta kasar. Tarrayar Najeriyar na tsakanin neman ingantar tsarin demokaradiyyar da ke tangal tangal a cikin yankin yanzu da kuma kaucewa shiga rudani cikin kasar da hankalin al'umma ke a rabe bisa turbar addini da kabila.