Najeriya: Buhari ya gana da gwamnonin APC
February 3, 2023A cigaba da kokarin kare rikicin da ke barazana ga makomar jam'iyar APC mai mulkin Najeriya, gwamnonin jam'iyyar 22 sun gana da shugaban kasa da nufin gano bakin zaren warware matsalolin da ke tattare da sabon tsarin fasalta kudin Najeriya da ya janyo kace-nace. A tozalin da gwamnonin suka yi da shugaba Muhammadu Buhari, a karon farko wasu gwamnonin da ke zargin wasu masu fada a ji a fadar gwamnatin kasar da kokarin cika burinsu na kauda masu tsintsiya daga mulki a yayin babban zaben da ke tafe, ta hanyar amfani da batun sauyin kudin naira da ke ci gaba da tada kura.
Karin Bayani: An tsawaita wa'adin karbar tsoffin kudi a Najeriya
Ganawar da ta dauki awowi kusan biyu ta kare tare da alkawarin shugaban kasar na shaida wa gwamnonin cewar yana shirin sauraron bangarorin da ke rikicin kafin yanke hukuncin da yake ganin ya dace a matsayin mafita ga rikicin da ya dau sabon fasali irin na siyasa. Babbar fargabar da ta mamaye zukatan wasu kusoshin gwamnatin Muhammadu Buhari, ita ce jam'iyyar fuskanci fushi daga masu zabe a fadin kasar bayan bijiro da sabon tsarin na sake fasalin kudin Najeriya da ake dada kallo tamkar asara ga wasu miliyoyin 'yan kasar a halin yanzu.
Sai dai a fadar gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, "Abun da ke faruwa a yanzu, baya da wani tasiri ga tunanin 'yan Najeriya masu kada kuri'a."
Karin Bayani: Shirye shiryen zaben Najeriya ya kankama
Sannu a hankali rikicin sabon kudin Najeriya na neman rikidewa ya zuwa ga na siyasa mai zafi, wanda magoya bayan Shugaba Buhari ke zargin gwamnan jihar Kaduna da kokari na neman sabon ubangida. A baya dama Gwamna el-Rufa'i ya yi fada da Atiku Abubakar a lokacin da yake neman hada inuwa da Obasanjo, kafin daga baya ya zagi Obasanjon a kokarinsa na neman shiri da shugaban da ke mulkin Najeriya a yanzu, duk da yake gwamna el-Rufa'i ya nuna cewa, zarge-zargen hira ce kurum irin ta taburin mai shayi.