1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Najeriya 16 sun halaka a jihar Delta

March 17, 2024

Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojin kasar akalla 16 sakamakon far musu da aka yi a lokacin da suke aikin wanzar da zamana lafiya a wasu kauyuka biyu da ke karamar hukumar Bomadi a jihar Delta.

https://p.dw.com/p/4doV8
USA Soldaten aus afrikansichen Ländern bei der Militärakademie in Jacqueville
Hoto: Issouf Sanogo/AFP

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar tsaron Najeriya birgediya Tukur Gusau ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 14.03.2024 a lokacin da aka tura sojojin da nufin kwantar da wani rikici kan filayen noma da ya barke tsakanin mazauna kauyukan Okuama da Okoloba, sai dai matasa yankin dauke da bindigogi sun yi musu kawanya, lamarin da ya bar baya da kura.

Rundunar tsaron Najeriyar ta kuma kara da cewa, a lokacin da aka far wa sojojin an aike da wata bataliyar sojoji domin ta kai musu dauki,sai dai su ma ba su sha ba, inda 'yan bindigan suka halaka Kwamandan bataliyar da Manjo guda biyu da Captine guda da kuma sojojin daga 12.

Babban habsan sojan Najeriya janar Christopher Musa ya yi tir da lamarin tare da ba da umurnin gaggauta gudanar da bincike. A yanzu haka ma dai jami'an tsaron kasar sun bazama a kauyukan karamar hukumar ta Bomadi da ke jihar Delta domin farautar masu hannu a lamarin inda tuni wasu daga ciki suka shiga hannu.