1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmakin Turkiyya kan Kurdawan Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 17, 2019

Tun bayan da dakarun Turkiyya suka fara kai farmaki a kan Kurdwan Siriya da ke kan iyakar kasar da Siriya, matakin shugaban kasar Turkiyyan Recep Tayyip Erdoğan na kai farmakin ke shan suka.

https://p.dw.com/p/3RTGu
US und türkische Truppen Syrien
Sojojin Tukiyya sun kaddamar da hare-hare ta sama da ta kasa a kan iyakar kasar da SiriyaHoto: picture-alliance/AA

Shi dai Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya dade yana shan alwashin kai farmaki a kan Kurdawan da ke kan iyakar kasarsa da Siriya, wadanda ya bayyana matsayin barazana ga kasarsa. Erdoğan dai na zargin Kurdawan da ke yankin Arewa maso Gabashin Siriya da kuma ke kan iyaka da Turkiyyan da cewa, suna taimakawa Kurdawan kasarsa da ya ayyana a matsayin 'yan ta'adda.