1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Duniya na jinjina kan yarjejeniyar sulhun Hamas da Isra'ila

Abdoulaye Mamane Amadou
November 22, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yarjejeniyar tsagaita buda wuta da musanyar fursunonin da ake garkuwa da su tsakanin Hamas da Isra'ila, wata gaba ce mai matukar muhimmanci.

https://p.dw.com/p/4ZJd5
Antonio Guterres, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya
Antonio Guterres, sakatare janar na Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Brendan McDermid/REUTERS

Manyan kasashen duniya ciki har da Amurka da Rasha da Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da jinjina wa yarjejeniyar tsagaita buda wuta da musanyar fursunonin da ake garkuwa da su tsakanin Hamas da Isra'ila, tare da bayyana haka a matsayin wata gaba ce mai matukar muhimmanci, to amma sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai sauran rina a kaba game da cimma batun zaman lafiya.

Karin Bayani: Taron ministocin harkokin wajen G7 zai mayar da hanakali kan rikicin Isra'ila da Hamas

A cikin wata sanarwar da ya fitar, babban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya jinjina wa matakin da bangarorin da ke batakashi suka cimma, a karkashin jagorancin Katar da Masar da Amurka, tare da bayyana cewar majalisar za ta yi iya kokari na ganin an tabbatar da ita.

Karin Bayani:  Kasashen Larabawa da Musulmai sun fidda sanarwa kan rikicin Gaza

A tsakiyar dare ne gwamnatin Isra'ila ta kada kuri'ar amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar da kungiyar Hamas, wadda manyan kasashen duniya ciki har da Amurka da Jamus suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda, da zummar dakatar da luguden wuta a yanin Gaza, tare da musanyar fursunoni daga bangarorin biyu.