Fargabar tabarbarewar tsaro a Afghanistan
April 15, 2021Bayan kwashe tsawon shekaru 20 dakarun sojin Amirka na yakar mayakan Taliban na kasar Afghanistan, sabuwar gwamnatin kasar ta Joe Biden ta sanar da anniyar janye dakarun kasar baki daya daga cikin kasar. An tsayar da ranar 11.09.2021 a matsayin ranar da sojojin za su fice daga Afghanistan. Kusan shekaru ashirin da Amirka ta yi a Afghanistan ya zama yaki mafi tsawo da kasar ta yi. Bayan baiyana shirin janye sojojin, Amirka ta nemi kasashen Turai da suka mara mata baya a tura rundunarsu dpn yakar Taliban da suma su janye sojojinsu, tuni Jamus da Birtaniya da wasu kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO, suka yi na'am da kiran na Amirkan. Karin Bayani: Biden ya bayyana manufofinsa na ketare
Da yake jawabin sanar da ficewar Amirka Shugaba Joe Biden ya ce, an tura sojin Amirkan ne domin karya alkadarin Kungiyar al-Qaeda dama samar da adalci ga dubban mutanen da harin nan na 9/11 ya hallaka, wanda ya ce ya zuwa yanzu sun ci wannan nasarar saboda haka babu bukatar ci gaba da kashe biliyoyin kudi a kasar. Da dama daga cikin kasashen da ke wannan Kungiya NATO, sun fito sun bayana goyon bayansu karara ga Amirka. Ana ganin wannan wata dama ce da ka iya bai wa kasashe kamar su Pakistan da Indiya da Chaina gami da Rasha damar shiga domin biyan wasu bukatunsu da dama kasancewar Amirkan ne ya hana su rawar gaban hantsi. Karin Bayani: Sharhi: Amirka da Taliban ina aka kwana?
Masana a fanin tsaro na ganin wannan mataki na Amirka dana kungiyar kawancen tsaro taNATO, ba komai zai haifar ba illa bai wa 'yan Taliban damar da za su ci karensu ba babbaka, idan aka yi la'akari da cewar ko baya ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma da su a shekarar da ta gabata da kuma kasancewar sojin kawancen, mayakan na ci gaba da kai hare-harensu, tun bayan wannan sanarwar al'umma da dama a kasar ta Afghanistan na cike da fargabar halin da rayuwarsu za ta fada a muddun aka janye dakarun da ke ba su tsaro.