Arangama ta barke a yakin neman zaben Kwango
November 29, 2023Majiyoyi masu tushe daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun ce an halaka wani dan jam'iyyar adawa ta dan takararar shugabancin kasa Moise Katumbi a yayin wata aragama da ta barke tsankanin magoya bayansa da 'yan bangaren jam'iyya mai mulki a lokacin da yake yakin neman zabe a Gabashin kasar.
Karin bayani: Yakin neman zabe ya fara gudana a kasar Kwango
A cewar mai magana da yaun jam'iyar adawar an halaka mutumin ne da ke a matsayin shugaban matasa na UDPS a yayin da aka kai wa ayerin motocin da ke rakiyar Katumbi hari a lokacin isarsa Kivu babban birnin lardin Maniema. Kazalika kakakin ya kuma zargin gwamnan lardin da zama ummulhaba'isin arangamar da ta barke, inda ya nemi da a gagauta dakatar da shi domin ya fuskanci shari'a.
Karin bayani: An hana madugun adawa shiga Kwango
A daya gefe kuma kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da cewa masu sa ido sama da 40 da ta aike Kwango domin lura da zabukan da za a gudanar a ranar 20 ga watan Disamba mai kamawa ba su samu zarafin isa wasu sassan kasar ba saboda dalilai na tsaro.