Tattalin arzikin Jamus ya ja baya a 2023
September 28, 2023Kwamitin hadin gwiwa na hasashen tattalin arzikin wanda gwamnatin Jamus ta kaddamar da kuma ke fitar da rahotonsa sau biyu a kowace shekara, ya ce akwai yiwuwar daukacin abin da Jamus ke samu a shekara ya ragu 0.06% cikin dari a bana sabanin bayanan da ya fitar a baya wanda ya nuna kasar za ta sami matsakaicin ci gaban tattalin arziki na 0.03% cikin dari.
Karin Bayani: COVIFD-19: Koma bayan tattalin arziki a Jamus
Masana tattalin arziki sun ce tashin farashin makamashi a 2022 da ke da nasaba da yakin Rasha da Ukraine ya kawo nakasu ga farfadowar tattalin arziki da aka fara samu bayan annobar corona wanda hakan ke nufin kudaden da mutane ke da shi a hannu ba zai iya saya musu abubuwan da suke bukata ba, lamarin kuma da ya kawo cikas ga samar da kayayyakin masana'antu.