1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinibu ya bukaci Saudiyya da ta saka hannu jari a Najeriya

November 10, 2023

Shugaban Najeriya ya gayyaci masu hannu da shuni na kasar Saudiyya da su kara azama wajen saka hannu jari a kasarsa da ke zama kasa mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afrika.

https://p.dw.com/p/4YgZM
Tinibu ya bukaci Saudiyya da ta kara azama wajen saka hannun jari a Najeriya.
Tinibu ya bukaci Saudiyya da ta kara azama wajen saka hannun jari a Najeriya.Hoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika wannan tayi a yayin zaman taron Saudiyya da kasashen Afrika da ke gudana a birnin Riyad, inda ya bayyana fa'ida da amincin da ke tattare da saka hannun jari a Najeriya.

Karin bayani: Najeriya: Shirin inganta tattalin arziki

A daura da wannan kira shugaban Tinibu ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Saudiyya da Najeriya wacce ta jibanci karfafa huldar kasuwancin makamashi musanman ma Man fetur da Iskar gas da kuma musayar fasahohin kimiyar zamani.

Karin bayani: Najeriya ta nuna bukatar shiga kungiyar BRICS 

Tun bayan hawansa kan karagar mulki a watan Mayun da ya gabata, shugaba Tinibu ke kokarin aiwatar da sauye-sauye da nufin tada komadar tattalin arzikin Najeriya wanda ya samu gagarumar koma baya inda aka kamanta da shekarar 2014.

Karin bayani:  Yawan cinikin man Najeriya ya ragu