SiyasaTunusiya
Tunisiya ta dage ziyarar tawagar EU kan bakin haure
September 30, 2023Talla
A cikin wata sanarwa an ambato wani ministan kasar na cewa har yanzu da akwai rashin jutuwa tsakanin Tunisiya da hukumar Tarayyar Turai kan wasu muhunmnan batutuwa da ke kunshe a cikin yarjejeniyar da aka cimma a watan Yulin da ya gabata.
Karin bayani: Yarjejeniyar EU da Tunisiya kan 'yan gudun hijira
Daga nata bangare hukumar EU ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin na Tunisiya don sake tsayar da lokacin da ya dace don aike wa da tawaga domin kammala yarjejeniyar.
A karkashin yarjejeniyar dai EU ta yi alkawarin ba wa Tunisiya tallafi na kudin da ya kai miliyan 105 na Yuru domin tada komadar tattalin arzikinta, kuma ko da a tsakkiyar wannan mako hukumar ta sanar da ware wasu miliyan 42 na Yuru da za ta bai wa Tunusiyar cikin gaggawa.