Sabon rikicin 'yan gudun hijira a EU
March 5, 2020Tun bayan da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bude hanya ga 'yan gudun hijirar da ke jibge cikin kasarsa mafi akaasari wadanda rikicin Siriya ya tilasta musu barin gidajensu, tare da ba su damar su tafi inda suke so, kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai EU musamman ma Girka suka shiga halin tasku. Tuni ma dai Girkan ta nemi tallafi daga rundunar musamman ta tsaron kan iyakokin kasashen Turai wato Frontex, bayan da ta gaza shawo kan 'yan gudun hijirar da ke tururuwa zuwa kan iyakarta da Turkiyyan, da nufin samun damar shiga nahiyar Turai, duk kuwa da kokarin da ta yi na ganin ta dakile yunkurin nasu.
Rahotanni sun nunar da cewa jami'an tsaron kasar ta Girka sun yi amfani da barkonon tsohuwa da sauran hanyoyi na ganin sun hana 'yan gudun hijirar daga Turkiyya isa kan iyakar kasar, sai dai hakan ya ci tura, abin kuma da ya sanya mahukuntan kasar neman agajin rundunar ta Frontex. Tuni dai kasashe irin su Jamus suka nuna takaicinsu dangane da matakin na Erdogan na kyale 'yan gudun hijirar, duk kuwa da yarjejeniyar da suka cimma da shi na cewa zai tsare su a kasarsa tare da hana su karasawa Turan, inda suka ce yana kokarin yin amfani da batun 'yan gudun hijirar ne domin cimma wata manufa tashi ta daban.