Amnesty: Hukuncin kisa ya karu a duniya
May 29, 2024A rahotonta na shekara Amnesty International ta ce an kashe akalla mutane 1,153 a bara ta hanyar hille kai, ko ratayewa, harbi ko kuma sanya guba. An samu karin kashi 31 cikin 100 na mutanen da aka kashe, idan aka kwatanta da na shekara ta 2022 inda aka kashe mutane 883. Addadin da marabin da akai mizaninsa tun a shekara ta 2015 na kisan mutane 1634
Kasashen da ke kan gaba wajen aiwatar da hukuncin kisan su ne China Iran da Saudiyya
Daga cikin kasashe 16 da suka aiwatar da hukuncin kisa, Iran ta dauki kusan kashi uku cikin hudu akalla mutane 853 aka kashe, yayin da Saudiyya ke da kashi 15 cikin dari mda mutum 172 wanda aka hile wa kai. Somaliya na da akalla mutane 38, sai Amurka da mutum 16. Addadin sabbin hukuncin kisa da aka zartar a duniya a shekarar ta 2023 ya karu da kashi 20 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata zuwa mutum 2,428 a kasashe 52. Kungiyar kare hakkin bil' Adama ta Amnesty International ta yi imanin cewar har yanzu ana aiwatar da kisa a kan mafi yawan mutane a China saboda tsarin mulkinsu wanda komai a asirce ake yin sa haka ma batun ya shafi shafi Koriya ta Arewa da Vietnam, Max Maisauer kwararre na kungiyar kare hakin bil Adama a kan batun hukuncin kisa ya ce galibi a kan yanke wa mutanen hukuncin kisa a wadannan kasashe saboda safara miyagun kwayoyi
Yawanci a kan yanke hukuncin kisan ne a cikin kasashen saboda safarar miyagun kwayoyi
"Hukuncin kisa da ake yi a wasu kasashe ya kusan daukar matakai kamar na zubar da jini, misali wanda aka ambata a Iran, kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi rajistan hukuncin kisa a kalla 246 a shekarar 2020, amma a sabon rahotonmu mutane 853 aka kashe''
Wasu kasashen sun soke hukuncin kisa
.To sai dai duk da haka kasashe da dama na duniya sun yi watsi da hukuncin kisan a baya-baya nan. Babbar magatagarda ta Amnesty International reshen Jamus, Julia Duchrow ta ce Ƙasashe da yawa sun yin watsi da hukuncin kisa. Ta ce an daina yin kisa a Belarus, da Japan, da Myanmar da Sudan ta Kudu. Ya zuwa yanzu, kasashe 144 suka soke hukuncin kisa. A cikin hukuncin kisa, sama da kashi 60 cikin 100 ana aiwatar da sh ne bisa laifukan da bai kamata a hukuntasu ta hanyar hukuncin kisa ba a karkashin dokokin kasa da kasa, musamman laifukan muggan kwayoyi. Aƙalla an zartar da hukuncin kisan mutane 246 a Iran a cikin shekara ta 2020.