Cin hanci da karbar rashawa na karuwa a Najeriya
December 8, 2023Tun dai a ranar 31 ga watan Oktobar sheakarar ta 2003 ce Majalisar Dinkin Duniya ta kebe rana ta musamman don duba matakan yaki da cin hanci da karban rashawa tsakanin kasashen duniya. Inda a Najeriya bayan kafa dokokin hukunta masu zambartar kasar biye da kafa hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, irin su EFCC da ICPC, batun cin hanci da rashawa dai kullum sai kara samun gindin zama yake.
Cin hanci da karbar rashawa na karuwa a Najeriya duk da hukukomin yaki da cin hancin da aka girka
Tarihi dai ya nuna yadda gwamnatin da ta gabata ta yi nasarar kama manyan jami'an gwamnatin kasar ciki har' da ministoci da tsoffin gwamnoni waddan da ta samu da hanu dumu-dumu a harkar cin hanci da rashawa, inda wasun su ma kotu ta zartar musu da hakuncin daurin shekaru. To amma a bisani sai gwamnatin ta sako su da sunan ahuwa. 'Yan Najeriya da dama dai na tambaya kan yadda za'a ce shugabanin hukumomin da ke yaki da karban hanci, tare ma da masu kula da baitil malin kasar kan fuskanci shari'a a gaban kotuna sakamakon zargin cin hanci.
Najeriya na hasarar miliyoyin Naira sakamakon cin hanci da ya yi katutu a kasar
Masharhanta dai sun yi hasashen cewar Najeriya kan yi hasarar bilyoyin Naira a lokaci kankani sanadiyar cin hanci da karban rashawa wanda da ya yi katutu tsakanin 'yan kasar musamman manyan jami'an gwamnati, don haka suke kallon cewar muddin aka cigaba da wannan tafiya, to da alamu za'a kai gabar da kasar za ta kasa motsawa.