Ana dab da kawar da zazzabin cizon sauro a Afirka
November 24, 2023Talla
Hukumar dake kula da aiwatarda riga kafin (Gavi) ta ce yanzu haka dubban darurruwan alluran rigakafin na RTS,S, sun isa a Kamaru Alluran rigakafin na RTSS na zazzabin cinzo sauron wanda hukumar lafiya ta duniya OMS ta tabbatar da ingancinsu. wannan shi ne karo na farko da za a fara amfani da su. Hukumar riga kafin ta GAVI ta ce kasahen Burkina Faso da Laberiya da Nijar da Saliyo ana sa ran za su sami allurai miliyan 1.7 na rigakafin na RTS,S a cikin makonni masu zuwa. Yayin da wasu sauran kasashen Afirka za su samu a cikin watanni masu zuwa. A shekara ta 2021 mutane miliyan 247 suka kamu da cutar zazzabin cizon a duniya, yayin da sama da dubu 600 suka mutu da cutar yawanci a kasahen kudu da hamada.