1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

CBN na kona kudin ajiya don farfado da darajar Naira

April 18, 2024

Muhawara ta barke a Najeriya kan rawar da babban bankin kasar ya taka kan yadda darajar Naira ke kara farfadowa biyo bayan zargi da ake yi wa CBN na kokarin kona kudaden ajiya na kasar domin neman tallafawa Naira.

https://p.dw.com/p/4evy3
Darajar Naira ta fara farfadowa bayan da CBN ta kashe wani kaso na kudaden ajiya
Darajar Naira ta fara farfadowa bayan da CBN ta kashe wani kaso na kudaden ajiyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

A lokaci kalilan ne Naira ta tarayyar Najeriyar ta tashi daga kudi na uku mafi lalacewa a duniya ya zuwa mafi tasiri a  tsakanin kudade. Sai dai wata kafar kudade ta Bloomberg ta zargi babban bankin kasar da kokarin kona kudaden ajiya na kasar don neman tallafa wa Naira ta kasar. Miliyan 2000 na Dallar Amurka ne suka kone cikin tsawon wata guda cikin kudaden ajiya na kasar da suka dawo Dalar Amurka miliyan dubu 32 maimakon 34 da suke a farkon watan Maris 2024. Amma gwamnan CBN Oluyemi Cardoso ya ce rawar ta Naira na zaman rawa ta gwanaye, kuma bankin ba ya da niyyar komawa zuwa batun tallafa wa Naira ta kasar.

Karin bayanTsadar takardun kudaden waje a Najeriyai: 

Babban bankin Najeriya na daukan matakai don farfado da tattalin arzikin kasar
Babban bankin Najeriya na daukan matakai don farfado da tattalin arzikin kasar

Bankin CBN ya ce Dalar Amurka ta tafi wajen biyan basukan kasar, ba wai jefa ta a kasuwar hada-hadar kudin canji da sunan tallafa wa Naira ba. A yanzu makomar ta Dala miliyan 2000 na jawo muhawara tsakanin kwarraru. Ibrahim Shehu da ke zaman shugaban kungiyar habaka tattalin arzikin arewacin Najeriyar ya ce matsayin bankin ya fi kama da hankali cikin dambarwar.

Karin bayani: Darajar Naira za ta ja baya a 2024 - Bloomberg

Tun farkon watan Maris 2024 ne aka fara kallon sauyin takun Dala sakamakon matakin bankin CBN na sayar da kudin na Amurka ga kamfanonin canji na Najeiya. Sai a baya, an zargi kanfanin da taka rawa wajen hana Naira samun daraja da kasar ke fatan ya iya kaiwa ga sauyin lamura. Sai dai matakin a fadar Umar Garkuwa da ke sana'ar canjin a Abuja ya kare ne da kama hanyar rusa daukacin masana'atar canjin maimakon ingantar lamuran kudi a Najeriya.

Karin bayani: Amfani da EFFC don ceto Naira a Najeriya

Naira ta fara faduwa kasa warwas kafin ta farfado a makonnin baya-bayannan
Naira ta fara faduwa kasa warwas kafin ta farfado a makonnin baya-bayannanHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A farkon shekarar 2024 ne Nairar ta kasance a sahu daya da kudaden Peso na Ajentina da  Pam na kasar Lebanon kafin kamen wasu jami‘ai na kamfanin Binance guda biyu da kuma fara harka ta matatar Dangote. Abubakar Ali da ke sharhi kan batun tattalin arziki ya ce har yanzu da sauran tafiya kafin a saitakudin Naira. 'Yan Najeriya da daman gaske na fatan sake komawar Naira zuwa gidan jiya na iya inganta rayuwa da makomar miliyoyi 'yan kasa.