1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Najeriya: Filayen jiragen sama ne mafita?

January 9, 2025

A yayin da ake ci gaba a cikin karatun babu, jihohin Tarayyar Najeriya da daman gaske sun koma batun ginin filayen jiragen sama duk da kasa fara biyan mafi karancin albashin ma'aikata.

https://p.dw.com/p/4ozfG
Najeriya I Jigila | Jiragen Sama
Jigilar jiragen sama ba ta da yawa a wasu jihohin NajeriyaHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Duk da cewar dai an yi nisa cikin batu na talauci a mafi yawan jihohin Tarayyar Najeriyar, ana ma jan-ciki wajen biyan shi kansa sabon mafi karancin albashi. Sai dai daga dukkan alamu, jihohin kasar na gasar ginin sababbin filayen jiragen sama. Zamfara dai ga misali, na shirin kishe sama da Naira miliyan dubu 100 wajen ginin sabon filin jirgin sama. Jihar Ebonyi ma dai na shirin kisan wasu miliyan dubu 53 na Naira ta kasar, Bayelsa kuwa ta kashe Naira miliyan dubu 70 duk dai cikin batun ginin sababbin filayen jiragen na sama cikin kasar da talauci ke dada samun tagomashi tsakanin al'umma.

Najeriya | Filin jiragen sama
Ma'aiakacin filin jirgin sama, na bai wa jirgin da ke sauka umarniHoto: picture-alliance/JOKER

Duk da cewar dai yawan filayen jiragen saman ba su wuce 43 cikin  Najeriyar ba, a halin yanzu da damansu na share kura ba tare da samun fasinjoji ba balle jiragen da ke shirin daukar su. Can a Jigawa dai ga misali fasinjoji 1,448 ne suka iya hawa jirage a cikin watanni shida na farkon shekara ta 2022, a yayin da jihar ke kisan abun da ya kai Naira miliyan 300 a wata a kokarin tafiyar da harkokin filin jiragen saman. Can ma a jihohin Gombe da Kebbi dai, ta kai gwamnatin jihar biyan masu jiragen wani kaso na kudi kan hanyar karkatar da jiragen zuwa ga sauka a filayensu.

Najeriya: Sake bude filin jirgin sama na Abuja

Kokari na takara mai ciwo ko kuma dabaru cikin batun cin-hanci dai, ana ginin tasoshin na sama da idanun neman hanyar kwashe dukiya. Gwamnoni a jihohin kasar da daman gaske dai, na kwashe dukiyar al'umma walau cikin ginin gada ko kuma sabuwar dabarar ginin filayen jiragen sama. Farfesa Hussain Tukar Hassan dai na zaman kwararre kan harkar mulki, kuma ya ce da kamar wuya samar da filayen jiragen saman ya taimaka wajen batu na ci-gaba a jihohin. Ya zuwa yanzun dai ko a cikin manyan filayen jiragen saman a mallaki na gwamnatin tarayyar 22 dai, uku kacal da ke Kano da Abuja da can a birnin Legas ke da karfin tsayuwa da kafarsu.