1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya: Jonathan ya yi bankwana da PDP

Ubale Musa AMA(LMJ
May 12, 2022

A daidai lokacin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta rasa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, jam'iyyar ta sanar da yin watsi da tsarin karba-karba da ke a cikin tsarinta na zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/4BDAv
Tshohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan 11.11.2014
Tshohon shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/AP

Kafin yanzu gwamnoni da ragowar 'yan siyasa a kudancin Najeriya membobin jam'iyyar PDP sun ce ya zama wajibi takarar jam'iyyar ta fito daga kudancin kasar, bayan kamalla wa'adin gwamnatin APC  da shugabanta ya fito daga yankin arewacin Najeriya, har ma ta kai ga jiga-jigan jam'iyyar da mika jan ragamar shugabancin PDP ga wasu 'yan arewacin kasar, duk a yunkuri na samun takarar shugabancin kasa daga yankin kudancin Najeriya.

Karin Bayani: Rikicin takarar shugaban kasa a PDP

A yayin babban taron jam'iyyar da aka kammala a Abuja ya bude takara a tsakanin sassan arewacin kasar da kudancinta, matakin da ke nufin kawo karshen tsarin karba-karba da ya kunno kai a shekara 2007 mai cike da cece-kuce. Aminu Waziri Tambuwal shugaba kungiyar gwamnonin jam'iyyar ya bayyana cewa yankin arewacin Najeriya na bin jam'iyyar PDP bashi.

Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
Jam'iyyar PDP mai adawa a NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

"Mutanen Arewa a jam'iyyar PDP suna ganin cewa shekara 20 zuwa 24 in har Shugaba Buhari ya gama mulki, dan Arewa daga jam'iyyar PDP Malam Umaru Musa 'yar Adua shekaru biyu kawai yayi yana mulki, sauran shekarun duk 'yan kudancin kasar ne suka yi tsakanin Obasanjo da Jonathan. Saboda haka ne duk wani dan PDP daga arewacin Najeriya gani yake tamkar yana bin jam'iyyar PD bashi, kuma ya kamata a biyashi kafin ta dauki nata kaso".

Karin Bayani: Yawaitar 'yan takara shugabancin Najeriya

Wannan mataki na rushe tsarin karba-karba ya kara fitowa fili da guguwar da ke cikin jam'iyyar PDP wacce ta share shekaru da dama, kuma masu sharhi na ganin 'yan jam'iyyar PDP na fargabar kada su fuskanci hushin yankin arewacin kasar ne da ke iya sa su fadi zabe, kuma su jira har wasu shekaru masu tsawo da ke tafe. Comrade Saidu Bello jigo ne a jam'iyyar daga jihar Kano ya ce.

"Ba za mu bari a ringa kudunduno mana yan taka daga ta ko ina ba, wanda ya dace ko wanda bai dace ba kuma dole ku karbesu, idan kuma ya kasance a kan madafan iko sai ya dinga yin yadda yaga dama".

Wannan sabon tsarin na cigaba da burge masu kallon siyasa daga nesa, inda wasu ke cewa matakin na iya hada kan 'ya 'yan jam'iyyar ta PDP da ta jima tana adawa a Najeriya.