Najeriya: Za'a hana 'yan ta'adda shiga YouTube
August 5, 2022Karuwar amfani da shaffukan sadarwa wajen aikewa da sakwani na bidiyo musamman ta kafar YouTube da wadannan kungiyoyin ke yi a matsayin wata sabuwar dubara ta farfaganda da yada manufofinsu ya sanya fusknatar karuwar wadannan aiyyuka a Najeriya.
Tun daga haramtacciyar kungiyar masu ikirarain kafa kasar Biafra ta IPOB ya zuwa kungiyoyin Isawap da ma na Boko Haram dukkansu na amfani da kafofin sada zumunta na zamani don aikewa da sakwaninsu ga jama’a, lamarin da ya sanya kula wannan yarjejeniya da gwamnatin Najeriya ta yi da kamfanin Google.
Karin Bayani: Buhari na fuskantar barazanar tsigewa
Lai Mohammed minstana yada labaru da al’adun gargajiya na Najeriyar ya ce "Muna son kamfanin Google ya duba hanyara da zai iya dakile sakwanin bidiyo a shaffukan kungiyoyin ta’adanci ko wanda suke watsawa kai tsaye dama aika e-mail a tsakaninsu da masu dauke da sunayen kungiyoyin da aka haramta su dama dangoginsu wadanda suke a kafara sadarwa ta Google".
‘Yan Najeriya na cikin al'ummar duniya da ke yawan amfanin da hanyoyin sadarwa na ‘yanar gizo, domin bayanai sun nuna cewa kimanin yan kasar milyan 100 ne ke amfani da wadanann hanyoyin kana kuma daraktan kula da shiyyar Afrika na kamfanin Google Charle Murito ya ce "Google ya bullo da wani tsari na ganowa tare da dakile sakwanin da basu dace ba da ake yadawa ta kafarsu, ba za mu bari a yi amfanin da kafarmu ba domin cimma bukatar da bata dace ba".
Karin Bayani: Fargaba a zukatan 'yan Najeriya
Aiyyukan kungiyoyin ‘yan ta'adda na zama babban kalubale da ke fusknata Najeriyar, matsalar da sannu a hankali ke ci gaba da karuwa musamman amfani da kafar sadarwa ta ‘yanar gizo da don yada manufofinsu.